Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai

Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai

Wani matashin dan jarida, kuma mataimakin mai tace labarai a jaridar Brittle Paper, Otosirieze Obi-Young ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar Gwamna El-Rufai Hadiza isma El-Rufai.

Premium Times ta ruwaito Brittle ta sallami Young ne bayan ya yi wani rubutu da yake sukar Hadiza, bisa zarginta da yake yi da goyon bayan danta da ya yi barazanar yi ma mahaifiyar wani fyade.

Shugabar Brittle, Ainehi Edoro ta tabbatar da sallamar.

KU KARANTA: Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

Young ya tabbatar da sallamar, inda ya bayyana bakin cikinsa bayan kwashe tsawon shekaru hudu yana aiki da kamfanin.

Da fari dai rikici ne ya hada yaron Hadiza, Bello, da wani, wanda hakan yasa Bello ya fada ma abokin rikicin nasa bakaken maganganu, wadannan kalamai ne suka sa aka yi masa ca!

Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai a twitter
Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai a twitter
Asali: Facebook

“Ka fada ma babarka, zan yi amfani da ita, kuma har na rage ma abokaina a daren yau. Ban son jin ihun kabilar Ibo.” Inji Bello.

Daga cikin wadanda suka ja kunne Bello akwai tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, wanda ta nemi Bello ya fito ya nemi gafara, amma Bellon ya tsaya kai da fata a kan ra’ayinsa.

Wannan ne tasa aka nuna ma babarsa rubutun, amma koda ta gani, sai ta nuna ba wani abu bane idan Bello ya rama cin mutuncin da wasu ke masa a shafin sadarwa na Twitter.

Sai dai daga bisani bayan dogon muhawara, Hadiza ta nemi afuwan jama’a na rashin tsawata ma danta.

Da yake sanar da sallamar da aka yi masa, Young yace: “Shugabar kamfanin ta kira ni ta nuna damuwarta da rubutun da nayi da yadda na soki wani kamfanin jaridar Najeriya, sai na gyara rubutun na cire wannan sashin.“

“Ta sake kira na wai za ta sauke rubutun daga shafinsu, ni kuma na ga ba zan iya lamunta ba saboda an hana ni fadan ra’ayina, an sa ni na mayar da ra’ayina kamar wani rahoton labari,“

"Amma duk da haka bai isa ba. Daga nan sai na ce mata ta yi duk abinda za ta yi da rubutun." inji shi.

Washe gari Young ya tarar da an hana masa damar shiga shafin yanar gizon kamfanin, an cire shi daga masu kula da shafukan dandalin sadarwar kamfanin, daga nan yasan an sallame shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel