Sai kowace jaha a Najeriya ta samu rabonta na coronavirus – Shugaban NCDC

Sai kowace jaha a Najeriya ta samu rabonta na coronavirus – Shugaban NCDC

Shugaban cibiyar kula da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dr Chikwe Ihekweazu, ya yi amanna cewa kowace jaha a Najeriya za ta samu kasonta na annobar coronavirus.

Ihekweazu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a shirin safe na Channels TV wato Sunrise Daily.

Ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na kokarin ganin ta hana cutar yaduwa, inda ya ce hakan ya kasance babban aiki mai matukar wahala.

“Mun shawo kan cutar Lassa cike da nasara kuma babu wanda ya rufe kasar saboda babu bukatar yin hakan.

“Yanzu, COVID-19 ya fi girmama, a yanzu haka ya shiga jihohi 22 amma za ta shiga kowace jaha a Najeriya, babu dalilin da zai hana ta shiga – cutar numfashi ce,” in ji shugaban na NCDC a ranar Alhamis.

Ya kuma yi martani kan banbanci da aka samu a yawan adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 da NCDC ta saki, da kuma adadin a wasu jihohi, musamman a Lagas da Kano.

Dr Ihekweazu ya bayyana cewa hukumar lafiyar na ta aiki domin magance coronavirus, yayinda hukumomin jihohi na da nasu rawar ganin da za su taka.

Ya ce lallai Najeriya ba za ta iya guje ma annobar ba, sannan cewa NCDC za ta ci gaba da bayyana gaskiya wajen fadin sakamakon.

Sai kowace jaha a Najeriya ta samu rabonta na coronavirus – Shugaban NCDC
Sai kowace jaha a Najeriya ta samu rabonta na coronavirus – Shugaban NCDC
Asali: UGC

Shugaban na NCDC ya ce: “Yan kwanaki da suka gabata ne muka bude wajen gwaji a Kano. Don haka wadannan sun kasance sakamako na karin wararen gwaji da muke samarwa a kasar.“

“Gwaje-gwajen sun dan habbaka; ba zan iya cewa dari bisa dari ba amma sun kusa hakan. Mun samu karuwar yawan adadin wadanda suka kamu a rana daya.“

“Tun barkewar annobar, muna gwada mutane da yawa kuma hakan ya fara nunawa. Wannan shine iya abunda za mu iya yi daga NCDC, muna aiki tare da gwamnatocin jaha.“

“Sune ke da alhakin daukar mataki a matakan jaha, kuma duk muna bukatarsu dukka a yanzu. Ya zama dole mu fuskanci zahirin gaskiya cewa wannan annoba ce, wannan cuta ce.“

“Zai yadu a Najeriya, wannan haka yake ko shakka babu kuma hakkin da ya rataya a wuyanmu a matsayin kasa shine shiryawa sosai, domin cimma nasara wajen gano cutar, maganceta, jeranto wadanda suka kamu da kuma hana yaduwarta,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Tallafi 17 da Gwamnatin tarayya ta samu domin yaki da cutar COVID-19

A wani labarin mun ji cewa, hukumar NCDC, ta ce tana fuskantar manyan kalubale a fagen yaki da cutar covid-19 wadda ta zamto alakakai a sassan duniya daban-daban.

Shugaban hukumar Dr. Chikwe Ihekweazu, shi ne ya bayyana hakan da cewar yaga kwazo da nagartar ma'aikatar lafiyar kasar nan wajen lalubo wadanda ake zargi sun harbu da cutar corona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel