Mutanen Najeriya kusan 1000 su ka kamu da zazzabin Lassa a shekarar 2019

Mutanen Najeriya kusan 1000 su ka kamu da zazzabin Lassa a shekarar 2019

Jaridar nan ta Daily Trust ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna yadda mutanen Najeriya ke mutuwa a sakamakon kamuwa da cutar nan ta Lassa a cikin wannan shekarar.

Jama’a da-dama sun fi karkata a kan annobar COVID-19, sai dai abin da mutane ba su haroro ba shi ne, irin ta’adin da cutar Lassa ta ke yi, ya fi karfin na cutar Coronavirus a yau.

A shekarar bana wannan cuta ta zazzabin Lassa ta kashe akalla mutane 188 a Najeriya. Daga ciki har da likitoci shida, ban da kuma sauran ma’aikata da malaman asibitin kasar.

Rahoton ya nuna cewa daga Junairun 2019 zuwa farkon Afrilun nan, an samu mutane 963 da zazzabin Lassa ya kwantar. Cutar ta bayyana ne a jihohi 27 da ke cikin Najeriya.

Daga karshen watan shekaran jiya zuwa yanzu, an samu mutane 56 da cutar Lassa ta kashe. A daidai wannan lokaci kuwa mutane 373 ne su ka kamu da COVID-19 a kasar nan.

KU KARANTA: Masu jinyar COVID-19 sun koma lalata da junansu a Najeriya

Mutanen Najeriya kusan 1000 su ka kamu da zazzabin Lassa a shekarar 2019

Ana yakin COVID-19, Lassa ta na cigaba da kashe Jama’a rututu
Source: UGC

Daga cikin wadanda su ka kamu da wannan sabuwar cuta ta Coronavirus, mutane 11 ne su ka mutu. Wadannan alkaluma ba su taka kafar wadanda cutar Lassa ta kai barzahu ba.

Binciken da jaridar ta gudanar ya nuna cewa kusan 20% na wadanda su ka kamu da cutar Lassa su na mutuwa. A wani bangare kuma, kasa da 3% na masu COVID-19 su ke mutuwa.

Idan aka tattara jimillar mace-macen da aka samu a kasar daga cutar Lassa da kuma COVID-19 a wannan lokaci, za a ga cewa zazzabin Lassa ke da alhakin kashi 94.5% na mutuwan.

Annobar COVID-19 ta samu kashi 5.5% ne kacal na mace-macen da aka yi a wannan lokaci. Malaman asibiti 37 su ke kwance yanzu su na jinyar wannan zazzabi na ciwon Lassa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel