An sanar da mutuwar mai cutar covid-19 a Kano

An sanar da mutuwar mai cutar covid-19 a Kano

- An samu mutuwar mutum na farko da ke dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Kano

- Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta sanar da hakan a cikin wani takaitaccen sako da ta fitar a daren ranar Alhamis

- A cewar ma'aikatar, yanzu haka akwai jimillar mutane 21 da aka tabbatar da cewa su na dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar.

Ma'aikatar lafiya a jihar Kano ta sanar da mutuwar mutum na farko da aka tabbatar da cewa ya na dauke da kwayar cutar covid-19.

Ma'aikatar lafiyar ta sanar da hakan ne a cikin wani takaitaccen sako da ta wallafa a shafinta na Tuwita a daren ranar Alhamis.

Duk da ma'aikatar ba ta bayar da karin bayani a kan mai dauke da cutar da ya mutu ba, ta tabbatar da cewa yanzu haka akwai jimillar mutane 21 da su ka kamu da cutar a jihar, sabanin mutum 16 da NCDC ta bayyana.

Da yammacin ranar Laraba ne, cibiyar kula da cututtuka ma su yaduwa a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa an samu karin mutane 34 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2020.

DUBA WANNAN: Katsina: An fara bi gida - gida neman wadanda suka dawo daga Abuja da Legas

Cibiyar ta bayyana hakan ne a shafin ra'ayi na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane talatin da hudu (34) sun kamu da kwayar cutar covid-19 a jihohin Najeriya daban-daban kamar haka; 18 a Legas, 2 a Katsina, 12 a Kano, 1 a Delta, da 1 a Neja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel