Tinubu ya shawarci FG ta yi amfani da BVN wajen bawa 'yan Najeriya tallafin jin kai
Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, ya bukaci gwamnatin tarayya (FG) ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) wajen aika wa 'yan Najeriya kudin tallafin rage radadin matsin da annobar covid-19 ta haifar.
Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bayar da wannan shawara ne a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Laraba a Legas.
Ya ce za a iya biyan kudi kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci moriyar tallafin ta hanyar amfani da BVN dinsu.
Jagoran na APC ya kara da cewa za a fi samun tsaro ta hanyar tura kudi zuwa asusu tare da bayyana cewa hakan zai kawo karshen rigingimun da ake samu yayin rabon kudin hannu da hannu.
Tinubu ya ce yin hakan zai kara jawo dumbin jama'a, musamman talakawa mazauna kauyuka, su bude asusun banki.
"Akwai gidajen talakawa da ke bukatar abinci, ruwa, da sauran abubuwan more rayuwa. Akwai bukatar nuna tausayi ga irin wadannan mutane.
"Gidaje da dama a Najeriya su na bukatar tallafi domin yakar yunwa da kaucewa fadawa wahala," a cewar Tinubu.
Shawarar ta Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da samar wasu sauye - sauye a salon rabon tallafin jin kai da ta ke bawa talakawa da marasa karfi domin rage musu radadin matsin tattalin arziki da annobar cutar covid-19 ta haifar.
FG ta bayyana cewa za ta fara duba asusun bankin jama'a da kudin da suke kashewa wajen sayen katin waya domin sanin su waye ya dace ta bawa tallafinta na jin kai a zagaye na biyu na bayar da tallafin.
DUBA WANNAN: Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse
A cewar FG, duk wani dan Najeriya da ya ke da kudin da yawansu ya kai N5,000 a cikin asusunsa na banki ba zai samu tallafinta na jin kai da za ta raba a zagaye na biyu ba.
Kazalika, gwamnatin ta bayyana cewa akwai yiwuwar ba za ta bayar da tallafinta ga duk mai saka katin waya na fiye da N100 ba a rana.
A cewar ministar jin dadi da walwalar jama'a, Sadiya Umar Farouq, rabon tallafin jin kai zagaye na biyu zai mayar da hanakaline a kan talakawa da marasa karfi da ke zaune a kauyuka da maraya.
Da ta ke amsa tambaya a kan hanyar da gwamnati za ta bi wajen zakulo mutanen da su ka dace a bawa tallafin, ministar ta bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da lambar tantance asusun banki (BVN) da kuma layin wayar hannu na jama'a.
A wani jawabi da ta gabatar ranar Litinin, ministar ta bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni a kara adadin mutum miliyan daya a kan wadanda suka ci moriyar tallafin a zagaye na farko.
Tsarin shirin bayar da tallafin jin kai da gwamnatin tarayya ta fara ya na shan suka a wurin jama'a tare da saka babbar ayar tambaya a kan salon rabon tallafin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng