Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rage farashin takin zamani samfurin NPK da kashi 9.1 domin taimaka ma manoma.

Jaridar TheCables ta ruwaito gwamnan jahar Jigawa, Muhammadu Badaru ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Dutse a ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Ministar Buhari ta bayyana iya adadin yan Najeriya da zasu amfana da tallafin gwamnati

Gwamna Badaru, wanda yake shugabantar kwamitin shugaban kasa a kan harkar taki, PFI, ya ce gwamnatin ta dauki wannan mataki ne a matsayin tallafi ga yan kasa.

Gwamnatin ta rage 9.1% daga farashin buhun takin NPK mai nauyin kilo 50, a yanzu dai buhun NPK ya kai N5,500, amma sakamakon wannan ragin kashi 9.1, farashin ya dawo N5,000 kacal.

Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma
Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma
Asali: UGC

Dalilin wannan ragi da Buhari ya yi shi ne domin tallafa ma manoma tare da rage musu radadin mawuyacin halin da suka shiga a dalilin annobar Coronavirus, da sauran yan kasuwa.

“Da wannan muke sanar da manoma manufarmu na shirin tabbatar da wannan umarni na shugaban kasa nan bada jimawa ba. Za’a samar da isassun takin zamani a bana ta yadda zai isa jama’a duk kuwa da matsalar Coronavirus da muke sa ran ganin bayansa.” Inji shi.

A wani labari kuma, Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta yaba da matakin garkame jahar Kano da sanya takunkumi ga al’ummar jahar domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar.

Shugaban NLC reshen jahar Kano, Kabir Ado-Minjibir ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, a ranar Laraba.

A cewar Ado, NLC bata adawa da duk wani mataki da gwamnati za ta dauka domin kare yaduwar annobar Coronavirus a jahar Kano, asali ma tana goyon bayan ire iren matakan.

Gwamnan jahar Kano ya sanya ma jama’an Kano takunkumi ne sakamakon samun karuwan mutanen dake kamuwa da cutar Coronavirus a jahar Kano, domin kare cigaba da yaduwarta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel