Yanzu-yanzu: Coronavirus: An sake sallamar mutane 3 a Abuja

Yanzu-yanzu: Coronavirus: An sake sallamar mutane 3 a Abuja

Bayan sallamar mutane 9 da aka sallama jiya da dare, ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya sanar da cewa an sake sallamar wasu uku da daren yau Laraba, 15 ga Afrilu, 2020.

Ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita da yammacin nan misalin karfe 7:30.

Ministan yayi sanarwar ne yayinda ake sauraron sanarwa daga hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC kan adadin wadanda suka kamu da cutar yau Laraba.

Yace: "Ina farin cikin sanar muku da cewa an sallami karin mutane uku daga cibiyoyin jinya killacewarmu dake nan Abuja bayan sun samu waraka."

"Jimillan adadin wadanda aka sallama a birnin tarayya yanzu 23 ne."

Yanzu-yanzu: Coronavirus: An sake sallamar mutane 3 a Abuja
Yanzu-yanzu: Coronavirus: An sake sallamar mutane 3 a Abuja
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nasir El-Rufai ya bukaci alumma su yi watsi da labaran bogi da ake yadawa game da cutar COVID-19 da ta kama shi

Gabanin hakan, an sallami masu cutar Coronavirus 22 da sukayi jinya a jihar Osun da Legas bayan gwaji biyu daban-daban ya nuna cewa sun warke daga cutar.

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya bayyana cewa a jiharsa, sun sallami mutane shida.

Amma na Legas, Babajide Sanwoolu, ya bayyana cewa mutane 16 suka sallama ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu, 2020.

Gwamnan jihar Legas yace: “Ina da karin labari mai dadi daga cibiyoyin killacewanmu. Mun sallami mutane 16; maza 14, mata 2.“

“Daga cikinsu akwai Turawa 3 - Dan Birtaniya 1, dan China 1 da dan Poland daya.“

“Hakan ya kawo adadin mutanen da muka yi jinya kuma muka sallama zuwa 85.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel