Covid-19: Gwamnatin Neja ta hana tirela makare da jama'a shiga jihar

Covid-19: Gwamnatin Neja ta hana tirela makare da jama'a shiga jihar

Gwamnatin jihar Neja ta hana wata tirela makare da jama'a ta shiga jihar. Babbar motar ta taso ne daga jihar Legas.

Shugaban kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19, Ahmed Matane, ne ya jagoranci jami'an tsaron da su ka tsare motar a kan iyakar jihar.

Gwamnan jahar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sanar da rufe harkoki a jahar, inda ya kaddamar da hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na safe zuwa 8:00 na dare.

A cewar gwamnan dokar takaita zirga-zirgan ta fara ne daga ranar Laraba kamar yadda ya sanar a ranar Litinin, 23 ya watan Maris.

Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki sakamakon sabbin mutanen da aka samu sun kamu da cutar Coronavirus a Abuja, wanda jahar Neja ce mafi kusa da birnin tarayyar.

Covid-19: Gwamnatin Neja ta hana tirela makare da jama'a shiga jihar

Gwamnatin Neja ta hana tirela makare da jama'a shiga jihar
Source: Twitter

Amma a ranar 5 ga watan Afrilu, sai gwamnatin jihar Neja ta janye dokar ta baci da ta sanya a jihar inda aka haramtawa mutane zirga-zirga saboda tsoron yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

"A yanzu, an amince mutane su fita harkokinsu daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana."

DUBA WANNAN: Covid-19: An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

Sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin ko ta kwana a kan yaki da annobar Coronavirus, Ahmed Ibrahim Matane, ne ya sanar da hakan a Minna, yayin hira da manema labarai kan matakan da gwamnatin ke dauka wajen dakile cutar.

Ya ce za'a bude kasuwanni daga karfe 8 zuwa biyu kuma ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki amma zasu tashi karfe 2.

Ahmed Ibrahim ya kara da cewa gwamnatin ta gano hanyoyi 12 da mutane daga wasu jihohi ke iya shiga Neja kuma za'a cigaba da rufe iyakokin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel