Dokar zaman gida dole: An kama dan sanda yana karbar cin hanci a Legas

Dokar zaman gida dole: An kama dan sanda yana karbar cin hanci a Legas

Duk da a baya-bayan nan an cafke wasu 'yan sanda yayin da suke karbar na goro a hannun al'umma, an sake cafke wani dan sandan yana wannan mugun hali a jihar Legas.

'Dan sandan wanda jaridar This Day ta bayyana sunansa Musa, ta ruwaito yadda hoton bidiyo ya dauke shi yana tsaka da karbar cin hancin N7,000 a hannun wani direba domin ba shi hanya.

Na'ura mai daukan hoto ta hasko jami'in a yayin da yake karbar na goro a hannun direban domin ba shi damar wucewa a yankin Anthony na jihar duk da an shimfida dokar hana zirga-zirga.

Cikin bidiyon wanda ya karade zaurukan sada zumunta a ranar Talata, an hasko jami'in yana kidaya N7,000 da ya samu damar dafewa bayan sun kammala ciniki da direban.

'Yan sandan Najeriya a bakin aiki

'Yan sandan Najeriya a bakin aiki
Source: Twitter

Direban motar wanda ya tsinci kansa cikin hali na dugunzuma, ya shaidawa manema labarai yadda ta kaya tsakaninsa da jami'in dan sandan.

Ya ce "a yayin da nake kan hanyar zuwa asibitin Ikeja daga Lekki, sai kwatsam wani jami'in dan sanda mai suna Musa ya tsayar dani kuma ya bukaci sai na biya N20,000 ba tare da wani dalili ba."

"Bayan na nuna shaidar takardun asibitin ne daga bisani sai ya karbi N7,000."

A ranar Litinin da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tsawaita wa’adin kwanakin tilasta zaman gida a birnin Abuja, Legas da Ogun da kwanaki 14.

KARANTA KUMA: Tunawa da harin Nyanya: Mutane sun koka da rashin kulawar gwamnati

Hukuncin shugaban kasar ya biyo bayan ci gaba da karuwar adadin mutane wadanda suka kamu da cutar corona a Najeriya wadda ta zama ruwan dare a fadin duniya.

Ana iya tuna cewa, a shekarar 2013 ne rundunar 'yan sandan Najeriya ta kori wani dan sanda wanda aka dauki hoton bidiyonsa yana kokarin karbar cin hanci daga wajen wani mai mota.

Dan sandan ya yi kokarin karbar naira dubu ashirin da biyar a hannun wani mai mota, wanda ya saba ka'idar tuki daura da filin saukar jiragen sama a Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel