An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

An harbi wani matashi yayin da dandazon mata da matasa su ka fito domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsawaita dokar hana fita a karamar hukumar Sapele da ke jihar Delta.

Matashin da aka harba ya na daga cikin daruruwan fusatattun matasa da mata da su ka fito gudanar da zanga-zangar nema a basu tallafin jin kai tunda aka kara wa'adin sati biyu a kan dokar kulle da hana jama'a fita.

Duk da an samu rudani a kan harbin matashin, majiyar jaridar 'The Nation' ta rawaito cewa daya daga cikin jami'an tsaro da suka zo domin kwantar tarzoma ne ya harbe shi.

Majiyar ta bayyana cewa an garzaya da matashin zuwa wani asibiti domin ceton ransa.

"Jami'an tsaro sun zo wurin domin tarwatsa ma su zanga - zangar. Ina jin a kokarin tarwatsa jama'ar ne su ka harbi matashin a kugu," a cewar majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta.

Yayin zanga - zangar, fusattaun matasan sun dinga rera wakar "a bamu abinci, "ba zamu saurari duk wani zance ba".

A ranar Talata ne gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya fitar da sanarwar kara sati biyu a kan dokar hana fita daga gida da taron jama'a biyo bayan karewar wa'adin sati biyun farko da ya ayyana.

An harbi mutum daya yayin da mata da matasa su ka fito zanga-zangar hana fita a Delta

Mata da matasa sun fito zanga-zangar hana fita a Delta
Source: UGC

Da ya ke rokon jama'a a kan su bi umarnin hukuma da yin biyayya ga dokokin da ta gindaya, Okowa ya ce karin satin biyun za su taimaka wajen zakulo wadanda suka yi mu'amala da mutane uku da aka tabbatar su na dauke da cutar covid-19 a jihar.

DUBA WANNAN: FG ta janye shirin bayar da tallafin N20,000 a jihohi hudu

Kazalika, gwamnan ya bawa jama'ar jihar tabbacin cewa za a raba musu kayan abinci zuwa karshen makon da mu ke ciki.

Amma, fusattatun ma su zanga - zangar sun bayyana cewa mugunta ce ta sa gwamnati ta kara tsawon wa'adin dokar zama a gida bayan ba su da wutar lantarki da abinci a gidajensu.

Masu zanga - zangar da yawancinsu ke sanye cikin jajayen kaya, sun bayyana cewa gwamnati ba ta damu ko yunwa za ta kashesu a gidajensu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel