Najeriya ta bayyana rashin jin dadi kan cin zarafin 'yan kasarta a China saboda coronavirus

Najeriya ta bayyana rashin jin dadi kan cin zarafin 'yan kasarta a China saboda coronavirus

Gwamnatin Najeriya karkashin jagoracin shugaba Muhammadu Buhari, ta bayyana rashin jin dadinta dangane da cin zarafin 'yan kasar nan da ake yi a birnin Sin.

BBC Hausa ta ruwaito gwamnatin Najeriya yayin da ta ke bayyana bacin rai game da cin zarafi da kuma wulakantaswa da ake yiwa 'yan kasar nan da wasu bakaken fata 'yan Afirka a China.

Geoffery Onyeama, ministan harkokin waje na Najeriya, ya ce kasar ba ta ji dadin labarin da ta samu ba kan wariyar launi da ake yiwa bakaken fata a kasar China sanadiyar cutar corona.

A yayin zantawarsa da takwaransa na kasar China, Zhou Pingjian, Mista Onyeama ya yi tir gami da alla-wadai dangane da irin wulakancin da ake yiwa bakaken fata a China.

Ganawar ministocin biyu ta biyo bayan wasu rahotanni da suka bayyana yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga gidaje da kuma dakunansu na haya da suke zaune.

Ministan harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama

Ministan harkokin wajen Najeriya; Geoffery Onyeama
Source: Depositphotos

Kazalika ganawar ta su ta biyo bayan ci gaba da yaduwar jita-jita kan yadda ake zargin 'yan Afirka ko kuma bakaken fata na dauke da cutar corona.

Babu shakka wasu hotuna tare da faifan bidiyo masu sanya damuwar zuci, sun yadu a kafafen sada zumunta da ke bayyana yadda jami'an tsaron kasar China suke cin zarafin bakaken fata.

Wannan lamari ya sanya Najeriya ta ke jan hankalin gwamnatin China tare da bayyana bacin ranta da nuna rashin amincewa kan cin zarafin 'yan kasarta da ake yi inji Mista Onyeama.

Sai dai fadar gwamnatin kasar China da ke birnin Beijing, ta bayyana rashin jin dadinta kan wannan batu a cewar Mista Zhou.

KARANTA KUMA: Barazanar Kyanda ka iya biyo bayan cutar corona - UNICEF

Mista Zhou yayin jaddada muhimmancin bin diddigin wannan lamari, ya ce kasarsa ba za ta manta da alheran da ta ke samu daga Najeriya ba musamman a wannan lokaci.

A farkon wannan mako ne wasu mazauna Guangzhou 'yan kasar Afirka suka bayar da shaidar irin cin zarafin da suke fuskanta na fatattaka daga muhallansu.

Wannan lamarin ya sanya Amurka ta gargadi 'yan kasarta bakaken fata da su kauracewa garin.

Wasu majiyoyin rahotanni sun yi ikirarin yadda ake yiwa bakaken fata 'yan Afirka gwajin cutar corona tare da killace su na tsawon makonni duk da cewa ba su nuna alamun kamuwa da cutar ba.

Legit.ng ta fahimci cewa, tabbas kasar China ita ce mabubbugar samun barkewar cutar korona, sai dai alkalumma sun ce a yanzu kasar ta samu saukin yaduwarta daidai gwargwado.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel