Da duminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar CAC da ke Abuja

Da duminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar CAC da ke Abuja

Gobara ta tashi a hedikwatar hukumar yi wa kasuwanci rijista ta kasa (CAC) da ke unguwar Maitama a birnin tarayya, Abuja.

SaharaReporters tarawaito cewa wutar gobarar ta babbake hawa na karshe a ginin ofishin hukumar CAC mai bene hawa bakwai, tare da lalata muhimman kayayyaki.

Duk da ya zuwa yanzu ba a san dalilin tashin gobarar ba, jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin domin kashe wutar.

Da duminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar CAC da ke Abuja
Gobara a hedkwatar hukumar CAC da ke Abuja
Asali: UGC

A makon jiya ne karamin ministan kasafi da tsare - tsare na kasa, Prince Clem Agba, ya yi magana a kan gobarar da ta tashi a ofishin babban akawu na kasa inda ake zargin ta tafka barna a ginin ofishin da ake kira da 'rumbun ajiye kudin kasa (treasury house)'.

"Mu na wani taro na wasu ministoci da mambobin majalisa lokacin da labarin tashin gobarar ya same mu, kuma nan da nan na nemi a yi min uzuri don na garzayo na ga halin da ake ciki.

DUBA WANNAN: Fatima Garba: Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane

"Lokacin da na iso tuni jami'an hukumar kashe gobara na tarayya tare da hadin gwuiwar jami'an kashe gobara daga babbban bankin kasa (CBN) da jami'an kashe gobara na FCT da na wasu kamfanoni sun kashe wutar.

"Gobarar ta fara ne da misalin karfe 10 na safe, sakamakon haduwar wayar wutar lantarki a wurin kunna na'urar sanyaya daki da wani jami'i ya yi a hawa na hudu na benen gini.

"Mun duba sashen adana bayanai mun ga gobarar ba ta shafi bangaren ba, duk da ta taba dakin wasu na'urori da ke sanyaya wurin adana bayananmu.

"Ba mu kammala bincike da sanin barnar da gobarar ta yi ba, amma zan iya tabbatar muku da cewa duk bayanan da suka shafi harkokin kudi da hada-hadarsu, basu samu wata matsala ba," a cewar ministan yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan an kashe gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng