Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da tatsar albashin ma'aikata

Covid-19: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da tatsar albashin ma'aikata

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya bayar da umarnin dakatar da cire wani kasafi daga cikin albashin ma'aikata a jihar.

Bala Muhammad a gaggauce ya umarci babban akantan jihar da kuma masu ruwa da tsaki kan dakatar da tatsar albashin ma'aikatan jihar a matsayin gudunmuwarsu ta yakar cutar Korona.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni a ranar Litinin, 14 ga Afrilun 2020 yayin kaddamar da kwamitin habaka tattalin arzikin jihar a wannan yanayi na annobar cutar Korona.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, gwamnan yace wannan sabon hukunci ya biyo bayan korafen-korafen da wani rukuni na ma'aikatan jihar suka shigar.

A ranar Juma'a 3, ga Afrilun 2020, majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta yanke hukuncin cire wani kasafi daga albashin ma'aikatan jihar na watannin Afrilu, Mayu da kuma Yuni.

Gwamnatin Bauchi, Sanata Bala Muhammad, a bakin aiki

Gwamnatin Bauchi, Sanata Bala Muhammad, a bakin aiki
Source: Twitter

Majalisar ta yanke hukunci ne domin samun gudunmuwar yaki da cutar Korona, inda tayi nufin cire kaso 10% daga albashin sakatarori na dindindin da wadanda suke makamancin mataki.

Haka kuma ma'aikatan dake kan mataki na 16 da 17 za su bayar da gudunmuwar kaso 5% na albashinsu, inda za a cire kaso 1% daga albashin sauran ma'aikatan dake mataki na 1 zuwa 15.

KARANTA KUMA: Rikicin Tiv da Jukun: An rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Benuwe da Taraba

A ranar 24 ga watan Maris ne fadar gwamnatin Bauchi tare da sa hannun mashawarcin gwamnan kan yada labarai, Mukhtar M Gidado, ta tabbatar da cewa gwamnan ya kamu da cutar.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnan na Bauchi na daya daga cikin rukunin mashahuran mutanen da suka kamu da cutar Corona virus tun bayan da ta fara bulla a Najeriya cikin watan Fabrairu.

Sai dai babu shakka gwamnan ya samu waraka daga cutar bayan ya shafe tsawon makonni biyu yana jinya a killace kamar yadda ya bayyana da kansa a shafinsa na zauren sada zumunta.

A halin yanzu kamar yadda cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana, akwai mutane 373 da suka kamu da cutar corona a jihohi 20 cikin 36 dake kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel