Bello El-Rufai ya sha alwashin zuwa gaban kotu da wani ‘Dan Jarida

Bello El-Rufai ya sha alwashin zuwa gaban kotu da wani ‘Dan Jarida

A cikin makon nan ne aka samu ‘yar tsama tsakanin Bello El-Rufai da wani Bawan Allah inda har rikicin ya zama babban labari a jaridu da gidajen yada labarai na zamani.

A halin yanzu Malam Bello El-rufai, ‘dan gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya yi wa ‘dan Jaridar da ya buga rahoton rigimarsa da wannan Mutumi barazanar zuwa kotu.

Mista Samuel Ogundipe wanda ke aiki da gidan jaridar Premium Times, ya na cikin wadanda su ka buga labarin sa-in-sar da aka yi da Bello El-Rufai a dandalin Tuwita.

A ranar Litinin, 13 ga Watan Afrilu, 2020, Bello El-Rufai ya fito ya na zargin wannan ‘Dan jarida watau Samuel Ogundipe da zama Sojan hayan ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP.

El-Rufai ya fadawa Ogundipe cewa lauyoyinsa za su duran masa domin ya kare kansa na jifar sa da ya yi da barazanar fyade. Ya ce masa ya fara shirin kare kansa gaban kuliya.

KU KARANTA: Mai dakin El-Rufai ta dawo daga rakiyar Bello El-Rufai bayan kalaman fyade

Bello El-Rufai ya sha alwashin zuwa gaban kotu da wani ‘Dan Jarida
Bello El-Rufai ya fadawa ‘Dan Jarida ya saurari Lauyoyinsa
Asali: UGC

A cewar Malam Bello El-Rufai, ya na jiran ya ga jama’a sun fara kururuwar #FreeSamuel domin a saki wannan ‘Dan jarida, ma’ana idan Alkalin kotu ya bada umarnin ram da shi.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Samuel Ogundipe bai maidawa El-Rufai martani ba.

Kafin Ogundipe ya fito da wannan rahoto, ya bukaci jin ta bakin El-Rufai da Mahaifiyarsa.

Ogundipe ba bakon shiga kotu ko kuma zaman kaso ba ne. A Agustan 2018, ‘yan sanda sun sa kotu ta tsare wannan Mutumi amma daga baya aka bada belinsa a kan kudi N500, 000.

Ya ce: “Ya kai Samuel Ogundipe, Karen farautar PDP, kai ka cike mana gibin wasan na mu. Ina tabbatar maka da cewa Lauyoyina za su neme ka domin ka kare zargin amfani da barazanar fyade (da ka ce na yi). Nauyi ya na kanka. Ina jiran a fara yayata #FreeSamuel.”

Bello El-Rufai ya kare jawabinsa da cewa: “Nagode da ka karasa ragowar ladan.” El-Rufai ya yi wannan magana ne duk da a kan shafinsa na Tuwita a ranar Litinin da ta wuce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel