Annobar Coronavirus: Za mu ciyar da matasa 100,000 a kowane rana – Gwamnan Legas

Annobar Coronavirus: Za mu ciyar da matasa 100,000 a kowane rana – Gwamnan Legas

A kokarinta na rage ma jama’a radadin mawuyacin halin da ake a ciki sanadiyyar annobar Coronavirus, gwamnatin jahar Legas ta bullo da tsarin ciyar da matasa dubu 100 a duk rana.

Punch ta ruwaito gwamnan jahar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a fadar gwamnatin jahar dake Marina.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta gano sabbin mutane 119 dake dauke da alamomin COVID-19

Gwamnan yace za su samar da dakunan girke girken abinci a kowanne karamar hukuma dake jahar da nufin ciyar da matasa 100,000 abinci sau daya a kowanne rana.

“Za kuma mu biya mutane 250,000 kudaden tallafi wanda zamu zabo su daga cikin talakawa da gajiyayyun dake cikinmu wadanda suke da rajista da hukumar rajistan mazauna jahar Legas.” Inji shi.

Annobar Coronavirus: Za mu ciyar da matasa 100,000 a kowane rana – Gwamnan Legas
Annobar Coronavirus: Za mu ciyar da matasa 100,000 a kowane rana – Gwamnan Legas
Asali: UGC

Bugu da kari gwamnan ya bayar da umarnin sakin duk wasu motoci da ababen hawa da hukumomin gwamnatin suka kama tun daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2020.

Daga karshe gwamnan ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankulansu bisa karin wa’adin kwanakin 14 da gwamnatin tarayya ta yi musu a cikin dokar ta baci, inda yace:

“Karin kwanaki 14 zai baiwa jami’an kiwon lafiya daman gano duk masu dauke da cutar, tare da yi musu gwaji da kuma killace duk wadanda aka samu da ita.” Inji shi.

Jahar Legas ce dai kan wajen yawan adadin masu dauke da cutar Coronavirus, inda take da mutane 214 da annobar ta kama yayin da mutane 10 suka mutu a jahar duk a sanadiyyar cutar.

A wani labari kuma, Gwamnatin Saudiyya ta bayar da tallafin kayan abinci ga mutane 1000 a jahar Kaduna don rage musu radadin halin da suke ciki sanadiyyar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito Saudiyya ta bayar da tallafin ne ta hannun kungiyar Musulunci ta Duniya, tallafin ya hada ne da shinkafa, taliyar turawa da kuma man gyada.

An zabo mutanen ne daga unguwannin talakawa a Kaduna, kuma tsarin rabon ya nuna duk mutum ya samu buhun shinkafa kilo 1, katan na taliyar spaghetti da kuma man gyada lita 4.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel