Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

A cikin sakon sautin murya na minti 1 da dakika 42, Shekau ya bayyana cewa balai ne ba komai ba ya kawo cutar kuma shi da mutanen sa suna da maganin cutar.

A cewarsa maganin cutar ba komai bane sai sallah, ya kuma ce bullar cutar bai hana shi da mutanensa yin sallah ba tare da cudanya da juna kamar yadda Humangle ta ruwaito.

Ya kuma yi kira ga sauran mutane su tuba su dena aikata zunubai su rungumi sharia irin ta musulunci muddin suna son su kasance cikin lafiya.

Ga dai abinda wani sashi na sakon muryar ya ce, "Coronavirus! Kar ku zo ku lankaya wa wani abu, balai ne ya kawo cutan ko ta ina ya fito mu dai Allah ya kare mu, ga mu nan kuma muna sallah lokaci biyar.

"Muna yin Jumaa din, muna yin komin mu kuma muna hada zuciya, muna hada hannu kuma muna cin abinci a kwano daya. Lafiyan mu lau lau lau. Muna da antivirus, ku coronavirus ne ko naku, mu muna da anticoronavirus.

"Wanene shi, shine Allah, mu masu bautan Allah ne, ya fi dacewa ku sani idan ba ku sani ba. Muna cikin lafiya wallahi kuma wannan shine Allah, Alhamdullilahi."

Ya cigaba da cewa suna sallarsu tare da yin haddi na addinin musulunci.

Sakon muryar ta kuma ambaci kalaman batanci ga shugabanin kasashe kamar shugaban Amurka, Donald Trum, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, shugaba Idris Derby na Chadi ta tsohon shugaban kungiyar Muhammad Yusuf.

Daga karshe shekau ya yi kira ga shugabannin su tuba idan har suna son ya yabe su.

Ga dai cikakken sakon muryar a kasa kamar yadda Humangle ta wallafa.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram (Bidiyo)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel