Gwamnatin tarayya ta ce ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da aka tara ba

Gwamnatin tarayya ta ce ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da aka tara ba

Ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da hukumomi masu zaman kansu suka bayar don yakar cutar coronavirus ba.

A cewar NAN, ministan ya bayar da dalilan da yasa ba za a ba al’umman kasar kudin ba, a lokacin da ya bayyana a shirin “Politics Nationwide”, na Radio Nigeria a ranar Talata.

Ya yi martani ne ga wata bukata da ke naman a raba wa yan Najeriya wani bangare na kudaden domin su toshe gibin da dokar hana fita ya yi masu.

Ministan ya ce kudaden na inganta harkar lafiya ne, sannan cewa ba za a iya amfani dashi wajen samar da kayan rage radadi ba.

Gwamnatin tarayya ta ce ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da aka tara ba
Gwamnatin tarayya ta ce ba zata iya raba wa yan Najeriya kudaden tallafi da aka tara ba
Asali: UGC

Mohammed ya ce tawagar shugaban kasa kan coronavirus basu da iko a kan kudin, kuma cewa ba zasu iya raba wa kowa ko sisi daga kudin ba.

Ya ce a kokarin rage wa mutane radadi, kowace kasa na da tsarin da ta amince dashi wajen yin hakan.

Ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakai da dama domin rage wa mutane radadin COVID-19, wanda suka hada da raba kayan abinci, kudade da kuma dauke wa mutane biyan bashi.

Ya ce Najeriya ce kan gaba a Afrika ta bangaren rage wa al’ummanta radadi yayinda duniya ke yaki da annobar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An samu karin mutum daya mai Coronavirus a Kano

A gefe daya, Kungiyar gwamnonin yankin Arewa sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya agaza musu da kayan tallafi don raba ma jama’a da kuma cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong ne ya yi rokon a ranar Litinin bayan kammala taron gwamnonin da suka yi ta yanar gizo, inda yace da haka ne zasu iya yaki da cutar.

Cikin wata sanarwa da mashawarcinsa a kan harkokin watsa labaru, Makut Macham ya fitar, ya ce gwamnonin sun tattauna akan batutuwan da suka shafi COVID-19 da tasirinsa a Arewa.

A yayin ganawar, gwamnonin sun amince da hanyoyin da ya kamata su bi domin shawo kan wannann annoba wanda a yanzu haka ta kama kusan mutane 400 a Najeriya da kashe 10.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel