COVID-19 ta kashe Mara lafiya dan shekara 59 a Legas – Kwamishinan lafiya

COVID-19 ta kashe Mara lafiya dan shekara 59 a Legas – Kwamishinan lafiya

Wadanda cutar COVID-19 ta kashe a Najeriya sun kara yawa bayan da aka samu wani da cutar ta kai barzahu a farkon makon nan, Jaridar The Nation ta bayyana wannan.

Jaridar ta bayyana cewa gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da mutuwar wani Dattaijo. Gwamnatin ta bada wannan sanarwa ne ta bakin Kwamishinan kiwon lafiya.

Farfesa Akin Abayomi, wanda shi ne Kwamishinan harkar kiwon lafiya na jihar Legas ya bayyana cewa wannan cuta ta kashe wani dan shekara 59 ne da ya ke ta jinya.

Kwamishinan ya shaidawa Manema labarai cewa Marigayin ya ziyarci kasar Amurka kafin mutuwarsa. Wannan mutuwa ta sa wadanda cutar ta kashe su ka karu a Najeriya.

Mai girma Kwamishinan ya yi amfani da wannan dama wajen shaidawa jama’a cewa an sake samun wasu sababbin mutane 13 da ke dauke da kwayar wannan muguwar cuta.

COVID-19 ta kashe Mara lafiya dan shekara 59 a Legas – Kwamishinan lafiya
COVID-19 ta kashe Mara lafiya dan shekara 59 a Legas – Kwamishinan lafiya
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Najeriya da sauran Kasashen da su ka fi fama da tashin hankalin COVID-19

Abayomi ya kuma tabbatar da cewa mutane shida cutar ta kashe a jihar Legas. Kafin yanzu alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar da cewa cutar ta hallaka mutane 10.

Da wadannan mutane 13 da aka samu a jihar, wadanda su ke dauke da kwayar cutar Coronavirus a Legas sun koma 192. A Najeriya yanzu mutane 356 su ka kamu da cutar.

Fiye da rabin masu cutar Coronavirus su na Legas, haka kuma alkaluma sun tabbatar da cewa fiye da rabin wadanda su ka mutu a dalilin cutar sun fito ne dai daga Legas.

Fafesa Abayomi ya rubuta cewa: “Wani Namiji Mutumin Najeriya wanda ya dawo daga kasar Amurka kwanan nan ya mutu a sakamakon fama da cutar COVID-19.”

“Wannan ya sa yawan wadanda su ka mutu a sakamakon wannan cuta su ka kai mutane 6 a Jihar Legas.” Kwamishinan bai bayyana ainihin lokacin da ajalin ya auku ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng