'Yan bindiga sun kashe mafarauta 11 a Katsina

'Yan bindiga sun kashe mafarauta 11 a Katsina

- Mafarauta 11 ne suka rasa rayukansu a kauyukan Kaurawa, Gidan Goge, Tashar Tsamiya da Zan Bago na gundumar Pauwa da ke karamar hukumar Kankara

- Kakakin rundunar 'yan sandar jihar ya bayyana cewa, mafarautan tare da wasu 'yan sa kai ne suka shiga dajin inda suka kai hari ga 'yan bindigar

- Amma tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura rundunar hadin guiwa don binciko 'yan bindigar don su fuskanci hukunci

Mafarauta daga kauyukan Kaurawa, Gidan Goge, Tashar Tsamiya da Zan Bago na gundumar Pauwa da ke karamar hukumar Kankara ne aka kashe.

Ana ake zargin 'yan bindiga ne suka halaka mafarautan a yankin Dajin Giwa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, ganau ba jiyau ba sun ce an kashe mafarautan ne a daren Lahadin da ta gabata.

'Yan bindigar sun ritsa mafarautan a yayin da suka fita farauta a Dajin Giwa da ke kauyen Pauwa.

A take goma daga ciki suka rasa rayukansu yayin da guda daya ya mutu a babban asibitin Kankara a ranar Litinin.

Tuni dai aka mika wadanda suka ji rauni da kuma mamatan asibitin, cewar majiyar.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya ce takwas daga cikin mafarautan ne suka rasa rayukansu.

'Yan bindiga sun kashe mafarauta 11 a Katsina
'Yan bindiga sun kashe mafarauta 11 a Katsina
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

Ya ce mafarautan tare da wasu 'yan sa kai sun yi amfani da layu tare da sauran kayayyakin farautarsu inda suka shiga daji don kai hari ga 'yan bindigar.

Hakan kuwa ya jawo musayar wuta tsakaninsu don 'yan bindigar na shirye da miyagun makamai.

Ya ce, "A sakamakon haka, takwas daga cikin 'yan sakan ne suka rasa rayukansu. Wasu kuma sun samu raunika. Daga ciki akwai: Abdulaziz Bawa, Muntari Kaura, Nura da Yahaya duk daga tashar Tsamiya da kuma Umar Bawa."

Ya ce, a halin yanzu kwamishinan 'yan sandan jihar, Sanusi Buba ya tura rundunar hadin guiwa karkashin shugabancin DCP Suleiman Ketere don damko 'yan bindigar.

"Rundunar na kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu don jami'an tsaro na kokarin shawo kan lamarin," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel