Yadda annobar Coronavirus ta ke kashe Bayin Allah a kasashen Afrika
Daga lokacin da cutar nan ta Coronavirus ta bulla a Garin Wuhan da ke kasar Sin a shekarar bara zuwa yanzu, ta kashe mutane kusan 120, 000 a fadin kasashen Duniya.
A Nahiyar Afrika wadanda su ka kamu da cutar sun kai kimanin mutane 12, 000. Mutane kuma kusan 700 ne su ka sheka barzahu a sakamakon wannan cuta a Nahiyar
Legit.ng ta kawo rahoton yadda wannan annoba ta ke kashe Jama’a a kasashen na Afrika.
1. Aljeriya
Alkaluman da hukumomin Duniya su ka fitar ya nuna cewa Aljeriya ce kasar da ta fi kowacce fama da annobar COVID-19 a Afrika. Kawo yanzu mutane fiye da 1, 900 aka tabbatar sun kamu da cutar. Wadanda su ka mutu sun kai 313, amma akwai mutum fiye da 600 da su ka warke.
2. Masar
A kasar Misra da ke Arewacin Nahiyar, an samu fiye da mutum 2100 da su ka kamu da COVID-19. Daga ciki an rasa mutane 164, a daidai wannan lokaci kuma mutane 589 sun warke.
KU KARANTA: Hatsaniya ta barke a Legas bayan Gwamnati ta tsawaita zaman kulle
3. Maroko
A kasar Maroko, annobar COVID-19 ta hallaka sama da mutum 120 a yanzu. Haka zalika mutane 203 daga cikin fiye da 1, 700 da su ka kamu da wannan cuta sun samu sauki a asibiti.
4. Afrika ta Kudu
Sababbin alkaluman da su ka fito sun bayyana cewa Afrika ta Kudu ce kan gaba wajen yawan mutanen da su ka kamu da COVID-19. Cikin mutane 2, 272 da su ka kamu da cutar, 27 ne kacal su ka mutu. Daga cikin wadanda cutar ta kama, an samu mutane 410 da su ka warke.
5. Kongo
A jeringiyar da mu ka kawo, DR Kongo ce ta biyar. A wannan Kasa, COVID-19 ta ga bayan mutane 20. Mutane 17 ne kacal su ka warke daga cikin mutane 235 da su ka kamu da cutar.
A Najeriya dai akwai fiye da mutane 340 da aka gano su na dauke da kwayar cutar Coronavirus bayan an yi masu gwaji. Cutar ta kashe mutane 10, yayin da 91 su ka warke a kasar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng