Akwai yiwuwan iya daukan cutar Coronavirus ta tusa - Sabon bincike

Akwai yiwuwan iya daukan cutar Coronavirus ta tusa - Sabon bincike

Likitoci sun bayyana cewa za a iya yada cuta mai toshe numfashi wato Coronavirus (COVID-19) ta hanyar fitar da iska daga dubura wato tusa, Vanguard ta ruwaito.

Amma ba za a iya kamuwa da ita ba idan wanda yayi tusan na sanye da wando.

A Gwaje-gwajen da aka gudanar kan marasa lafiya, an samu cutar COVID-19 a cikin 'ba hayan' rabinsu.

Amma ana bukatan karin bincike kafin a iya watsi da zargin yiwuwan yada cutar ta tusa.

Wani Likita ya tada muhawarar a Soshiyal Midiya inda ya kafa hujja da binciken wani likitan kasar Australiya, Andy Tagg, ya gudanar.

A jawabin da kwararro, Dakta Tagg ya bayyana cewa a gwaje-gwajen da aka gudanar a farkon shekarar nan, an samu cutar cikin 'ba hayan' kashi 55% na masu dauke da cutar Coronavirus.

Likitan ya kara da cewa binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewa tusa na da karfin busa hoda.

Ya yi gargadin cewa idan mai cutar Coronavirus bai sanye da wando kuma yayi tusa, toh wani dake kusa idan ya shaka warin na cikin hadari.

“Da yiwuwan za a iya yada COVID19 ta tusa, muna bukatan karin hujja. Amma a koda yaushe a rika sanya kayan kare kai.“

KU KARANTA Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

Akwai yiwuwan iya daukan cutar Coronavirus ta tusa - Sabon bincike

Akwai yiwuwan iya daukan cutar Coronavirus ta tusa - Sabon bincike
Source: Facebook

A wani labarin daban, Kwamishanan lafiyan jihar Anambara, Dakta Vincent Okpala, a ranar Litinin ya bayyana cewa mutumin daya kawo Coronavirus jihar kuma ya gudu daga baya ya shiga hannu.

Kwamishanan ya bayyanawa manema labarai a Awka cewa an damke mutumin cikin inda ya boye kuma abin da ban takaici.

Ya ce an killace akalla mutane 29 wanda ya hada da ma'aikata kiwon lafiya, yan 'uwansa, da abokan huldansa.

Okpala yace “Mun nemi mutumin daga karfe 8 na dare zuwa 3 na dare bayan cibiyar takaita yaduwar cututtuka sun tuntubi gwamnatin jihar cewa sakamakon gwajinsa ya fito kuma ya kamu da cutar.“

“Tare da ni ake shiga wuraren da haka kawai ba zan shiga cikin dare ba, muna kwankwasa kofofin mutane muna tashinsu daga bacci domin nemansa.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel