An kashe tsohon shugaban karamar hukuma a Adamawa

An kashe tsohon shugaban karamar hukuma a Adamawa

- Wasu 'yan bindiga sun kashe tsohon shugaban karamar hukumar Ganye na rikon kwarya, Sabastine Kaikai, a sa'o'in farko na ranar Talata

- 'Yan bindigar dai sun je har gidan tsohon shugaban karamar hukumar da ke kauyen Kaikai na karamar hukumar Ganye

- Makwabtan tsohon shugaban karamar hukumar sun bayyana cewa ya yi kokarin tserewa amma sai suka kama shi tare da halaka shi a take

An kashe tsohon shugaban karamar hukumar Ganye na rikon kwarya, Sabastine Kaikai a sa'o'in farko na ranar Talata.

'Yan bindigar dai sun je har gidan tsohon shugaban karamar hukumar da ke kauyen Kaikai na karamar hukumar Ganye, inda suka aika dashi lahira.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta bayyana, har yanzu dai ba a san dalilin kisan nashi ba.

An gano cewa Sabastine Kaikai ya ziyarci kauyen ne don hutun bikin Easter amma sai ya iske ajalinsa bayan sa'o'i kadan da isarsa.

Kamar yadda makwabtansa suka bayyana, "Yan bindigar sun isa ne da tsakar dare inda suka fara harbin iska kafin su gaggauta shiga gidansa".

An kashe tsohon shugaban karamar hukuma

An kashe tsohon shugaban karamar hukuma
Source: UGC

DUBA WANNAN: Dokar hana walwala: An damke dan sanda ya karba cin hancin N40,000

Sun kara da cewa, "Ya yi kokarin tserewa daga gida amma sai suka kama shi. A take kuwa suka kashe shi har lahira".

Kamar yadda jami'in yada labarai na karamar hukumar Ganye, Kabiru Njidda ya sanar, ya ce da safiyar Talata ne ya tabbatar da cewa an kashe Sabastine.

Ya ce, "Gawar tsohon shugaban karamar hukumar na nan a ma'adanar gawawwaki da ke babban asibitin Ganye".

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje, ya ce rundunar tayi martani ta hanyar tura jami'anta don bibiyar makasan.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Audu Madaki, ya tura rundunar wajen karfe 5:30 na asuba don damko makasan.

Kwamishinan ya kara da cewa, makasan za su fuskanci hukunci matukar suka shiga hannu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel