Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo

Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo

Gwamnatin jahar Ondo ta sanar da samun wani sabon yaudwar annobar Coronavirus bayan cutar ta kama wani matashi mai yi ma kasa hidima, watau NYSC.

Punch ta ruwaito matashin dan bautan kasa yana yi ma kasa hidima ne a 32 Artillery Brigade daoe Owena, kuma ya kamu da cutar ne sanadiyyar mu’amala da wani dake dauke da ita.

KU KARANTA: Azumin bana babu Tafsiri a Masallacin Sultan Bello na Kaduna – Babban Limami

Da yake tabattar da aukuwar lamarin, kwamishinan watsa labaru na jahar Ondo, Donald Ojogo ya bayyana cewa matashin dan bautan kasa ne, kuma likita ne.

“Mutum na uku da aka samu dauke da cutar Coronavirus a jahar Ondo wani likita ne dake aikin bautan kasa a wani karamin asibitin Sojoji a cikin bariki, kuma ya kula da mutumin da ya fara kamuwa da cutar ne.

“Mai girma gwamna zai yi ma jama’a jawabi game da lamarin, kuma zai yi karin haske a kan mutumin.” Inji shi.

Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo
Da dumi dumi: Dan bautan kasa ya kamu da cutar Coronavirus a Ondo
Asali: UGC

A wani labarin kuma, Tun bayan bullar annobar Coronavirus, an samu sauye sauye da dama a al’amuran duniya gaba daya, wanda ya sauya salon tafiyar da hidindimu da yawa

A nan gida Najeriya ma wannan annoba ta kawo sanadiyyar sauya salon tafiya da al’amura, tun daga kulle makarantu, kulle kasuwanni, wuraren ibada da ma karya tattalin arziki.

Wannan tasa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Fitaccen Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng