Jam'iyyun siyasa sun kashe miliyan N800 a iya kotun koli

Jam'iyyun siyasa sun kashe miliyan N800 a iya kotun koli

Jam’iyyun siyasa da yan takararsu sun kashe kimanin naira miliyan 800 a kararrakin zaben da suka shigar kotun koli, inda suka bukaci a sake duba hukuncin da aka yanke.

Lauyoyin da suka hallara a zaman, sun bayyana cewa kudin kowani babban lauya da zai hallara a irin wannan zama na sake duba hukunci, kimanin naira miliyan 100 ne.

An tattaro cewa akwai kararraki hudu da aka shigar wanda suka bukaci a sake duba hukuncin kotun, sannan kowanne yana da manyan lauyoyi da suka hallara. Cikin haka sau biyu aka bukaci a sake duba hukuncin zabukan Rivers da Zamfara.

Daily Trust ta ruwaito cewa idan aka hada naira miliyan 100 da aka biya kowace jam’iyyar adawa a karar, hakan na nufin an kashe akalla naira miliyan 800 wajen sake duba karar.

Jam'iyyun siyasa sun kashe miliyan N800 a iya kotun koli
Jam'iyyun siyasa sun kashe miliyan N800 a iya kotun koli
Asali: UGC

Jam’iyyun siyasa a jihohin Rivers, Imo, Bayelsa da Zamfara ne suka nema a sake duba hukuncin da kotun koli ta yanke a kan zabukan 2019.

Sai dai kuma babu ko daya daga cikin masu karar da ya yi nasara, yayinda kotun koli ta sanya tara a kan lauyoyin da suka shigar da kararrakin jihohin Bayelsa da Zamfara.

Da yake magana kan lamarin, Obioma Ezenwobodo Esq, ya ce bai san ainahin nawa ake biyan lauyoyi a kan sake duba hukunci ba.

Sai dai ya ce ya san nau’in lauyoyin da ke hallara a kan wannan lamuran za su karbi kudin da ya kai haka ko ma fiye da hakan.

Da yake magana kan lamarin, Hamid Ajibola Jimoh Esq, ya ce kudin da ake biyan lauya kan haka kamar kwangila ne.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun tare dumbin matafiya a kan hanyar Lokoja zuwa Abuja

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon dan siyasa a jam'iyyar PDP, Farfesa Terhemba Shija ya sanar da barin jam'iyyar.

Farfesa Shija ya kasance a PDP ne tun a shekarar 1999 inda ya kasance jigo.

A wata wasika mai kwanan watan 8 ga Afirilun 2020, wacce aka mika ga shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Vandeikya, Farfesan yace ya fita daga jam'iyyar ne saboda dalilan kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel