Za a cigaba da zaman gida na tsawon makonni biyu a Ekiti – Gwamna Fayemi
A yunkurin takaita yaduwar cutar Coronavirus a jihar Ekiti, a jiya Litinin dinnan ne gwamna Kayode Fayemi ya kara wa’adin takunkumin da ya maka na hana fita a fadin jihar
Kayode Fayemi ya kara tsawon wa’adin zaman kullen da ake yi a jihar da makonni biyu. Gwamnan ya bada wannan sanarwa ne da Maraicen Ranar 13 ga Watan Afrilun 2020.
Sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Mista Biodun Oyebanji ya sa hannu a takardar da ta yi wannan jawabi. Mai girma gwamnan da kansa, ya fitar da wannan takarda a shafin Tuwita.
Sai dai gwamnan ya bayyana cewa za a saki marar jama’a a Ranakun Alhamis tsakanin karfe 6:00 na safe zuwa 2:00 na rana domin su samu damar sayen kayan abinci a kasuwa.
Haka zalika daga yau Talata, 14 ga Watan Afrilu, amfani da tsummar rufe fuska ya zama wajibi a cikin Bainar Jama’a. Wannan zai taimaka wajen rage yaduwar wannan cuta a Ekiti.
KU KARANTA: An tirke wasu Ma'aikata bayan COVID-19 ta kashe wata Mata a asibiti
Gwamnatin jihar Ekiti ta ce ta na kokarin samar da wadannan tsummokara da ake amfani da su wajen rufe fuskoki ga Ma’aikatan da aka ba damar fita aiki a irin wannan lokaci.
Da wannan mataki da gwamna Kayode Fayemi ya dauka, za a cigaba da koyar da ‘Yan makarantun Firamare da Sakandare ne ta kafar yanar gizo yayin da aka haramata cinkoso.
Gwamnan ya bayyana cewa haduwar mutum 20 a wuri guda bai halatta ba har yanzu a jihar Ekiti. Wadannan jerin dokoki sun fara aiki daga yau kamar yadda umarnin ya nuna.
Sauran matakan da gwamnatin Fayemi ta dauka tun a lokacin da aka fara haramta fita za su cigaba da aiki. Za a dabbaka wadannan matakai har zuwa Ranar 27 ga Watan Afrilu.
Idan ba ku manta ba a jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tsawaita wa’adin takunkumin da ya sa a jihohin Legas, Ogun da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng