Ka taimake mu da kudin tallafi da cibiyoyin gwajin Coronavirus – gwamnonin Arewa ga Buhari

Ka taimake mu da kudin tallafi da cibiyoyin gwajin Coronavirus – gwamnonin Arewa ga Buhari

Kungiyar gwamnonin yankin Arewa sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya agaza musu da kayan tallafi don raba ma jama’a da kuma cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus.

Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong ne ya yi rokon a ranar Litinin bayan kammala taron gwamnonin da suka yi ta yanar gizo, inda yace da haka ne zasu iya yaki da cutar.

KU KARANTA: Buhari ya ce babu shiga babu fita a Legas da Abuja, amma zasu cigaba da raba kudade

Cikin wata sanarwa da mashawarcinsa a kan harkokin watsa labaru, Makut Macham ya fitar, ya ce gwamnonin sun tattauna akan batutuwan da suka shafi COVID-19 da tasirinsa a Arewa.

A yayin ganawar, gwamnonin sun amince da hanyoyin da ya kamata su bi domin shawo kan wannann annoba wanda a yanzu haka ta kama kusan mutane 400 a Najeriya da kashe 10.

Ka taimakemu da kudin tallafi da cibiyoyin gwajin Coronavirus – gwamnonin Arewa ga Buhari
Ka taimakemu da kudin tallafi da cibiyoyin gwajin Coronavirus – gwamnonin Arewa ga Buhari
Asali: Twitter

“Bayan samun rahotannin jahohi daban daban, kungiyar ta kuduri tsaurara matakan rigakafi ta hanyar kulle iyakokin jahohi, sanya idanu da kuma aiki tare wajen takaita zirga zirga a tsakanin jahohin.

“An kuma tattauna batun tallafi, inda suka ce har yanzu babu wata jaha daga yankin da ta samu ko sisi daga gwamnatin tarayya duk da cewa an samu bullar cutar a wasu jahohi, yayin da wasu ke kokarin kare kansu.

“Gwamnonin sun koka kan yadda kokarin da suke yi na yaki da cutar ta tatuke lalitarsa, don haka suke ganin ba lallai su iya cigaba da iya kashe kudade a kan cutar ba, don haka kungiyar ta amince ma shugabanta ya gana da gwamnatin tarayya domin samun tallafi.” Inji sanarwar.

Haka zalika kungiyar ta yanke shawarar tuntubar gwamnatin tarayya domin samar da cibiyoyin gwaje gwajen cutar a kowacce jahar dake Arewacin Najeriya.

Wannan tasa ta kafa kwamitin mutane bakwai a karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu domin lalubo hanya mafi inganci da ya kamata ta bi.

Daga karshe kungiyar ta jinjina ma shugaba Buhari bisa matakan da gwamnatinsa take dauka don dakile yaduwar cutar, tare da alkawarin aiki da gwamnatin tarayya don samun nasara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng