Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga al’umman Najeriya a yau Litinin

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai yi jawabi ga al’umman Najeriya a yau Litinin

- Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya a yau Litinin, 13 ga watan Afrilu

- A sanarwar da fadar shugaban kasar Najeriya ta a shafinta na Twitter, ta ce Buhari zai yi jawabin ne da karfe 7:00 na yamma

- An bukaci gidajen talbijin, na radiyo da sauran kafofin watsa labarai su jone da tashar NTA da radio Nigeria domin jin jawabin nasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga al’umman Najeriya a yau Litinin, 13 ga watan Afrilu. Zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma.

Fadar shugaban kasar Najeriya ce ta fitar da sanarwar a shafinta na Twitter.

An bukaci gidajen talbijin, na radiyo da sauran kafofin watsa labarai su jone da tashar NTA da radio Nigeria domin jin jawabin shugaban kasar.

Ana dai tunanin jawabin shugaban kasar zai kunshi batun annobar coronavirus ne da kuma matakan da gwamnati ke dauka.

Ana kuma sanya ran watakila shugaba Buhari ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jihohin Legas da Abuja da kuma Ogun.

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa ta yi umurnin bude makarantu.

Ma’aikatar ilimi ta tarayya a cikin wani jawabi daga kakakinta, Ben Goong, ta bayyana ikirarin cewa gwamnati ta yi umurnin bude makarantu a matsayin labaran karya.

Goong ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar cewa ministan ilimi, Adamu Adamu, ya yi umurnin bude makarantu.

Ya shawarci iyaye da waliyai da kada su bari a rude su da labaran karya, sannan cewa su bi umurnin gwamnatin tarayya domin magance annobar COVID-19.

“Kan batun bude makarantu, ma’aikatar bata yi umurnin bude kowani makaranta a kowani mataki ba. Jawabin da aka saki da sunan ma’aikatar karya ne domin bai fito daga ministan ba.

“Ana shawartan iyaye, dalibai da al’umma da su yi watsi da labaran karyan da aka saki,” in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel