Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi

Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi

Wasu gungun yan bindiga dadi sun kaddamar da mummunan hare hare a karshen makon da ta gabata a kauyen Sabon Layin Galadima dake cikin karamar hukumar Faskari ta jahar Katsina

Daily Trust ta ruwaito da misalin karfe 5 na asuban jiya yan bindiga suka shiga gidan wani manomi, Buhari Umaru, inda suka kashe shi nan take ba tare da daukan komai a gidansa ba.

KU KARANTA: Annobar Corona: Sultan ya bayyana bacin rai da yadda gwamnoni suka bude wuraren ibada

A ranar Juma’a ma yan bindiga sun bude ma wata mota wuta a kan hanyar Faskari daga Sabon Layi makare da Fasinjoji da kaya, inda suka kashe karamin yaro, suka jikkata uwarsa.

Shaidu sun bayyana a kullum ana kai ma jama’a hari tare da musu fashi, musamman ma satar babura, wanda ya zama ruwan dare, kuma miyagun suna fakewa ne a cikin dazuka.

Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi
Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi
Asali: UGC

A hannu guda, mutane 7 sun mutu da yammacin Lahadi, 12 ga watan Afrilu yayin da yan Boko Haram suka kai harin kwantan bauna a kan wasu motocin haya guda 2 a jahar Borno.

Boko Haram ta tare motocin ne a wajen garin Auno, kimanin kilomita 20 daga garin Maiduguri, a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

A kwanakin baya ne gwamnatin jahar Borno ta sanya dokar takaita zirga zirga a kan hanyoyin shiga da fita jahar don kare yaduwar Coronavirus, illa babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Sai dai a yanzu, kwamitin ko-ta-kwana a kan COVID-19 dake karkashin Umar Kadafur ta sanar da garkame hanyar ita ma, kuma dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin.

Wani matafiyi da ya yi ido hudu da gawarwakin ya bayyana cewa ya kirga gawarwaki guda 7 a wajen garin Auno, kuma an fada musu a daren jiya aka kai harin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel