COVID-19: Gwamnatin tarayya ta ce ba yanzu za a bude makarantu ba

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta ce ba yanzu za a bude makarantu ba

- Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta yi watsi da ikirarin cewa ta yi umurnin bude makarantu

- Ma’aikatar ilimi ta tarayya a wani jawabi da ta saki, ta bayyana ikirarin cewa gwamnati ta yi umurnin bude makarantu a matsayin labaran karya

- Ma’aikatar ta bukaci yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar da ta yi zargin cewa ministan ilimi, Adamu Adamu ya yi umurnin bude makarantu

Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa ta yi umurnin bude makarantu.

Ma’aikatar ilimi ta tarayya a cikin wani jawabi daga kakakinta, Ben Goong, ta bayyana ikirarin cewa gwamnati ta yi umurnin bude makarantu a matsayin labaran karya.

COVID-19: Gwamnatin tarayya ta ce ba yanzu za a bude makarantu ba
COVID-19: Gwamnatin tarayya ta ce ba yanzu za a bude makarantu ba
Asali: Facebook

Goong ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar cewa ministan ilimi, Adamu Adamu, ya yi umurnin bude makarantu.

Ya shawarci iyaye da waliyai da kada su bari a rude su da labaran karya, sannan cewa su bi umurnin gwamnatin tarayya domin magance annobar COVID-19.

Kan batun bude makarantu, ma’aikatar bata yi umurnin bude kowani makaranta a kowani mataki ba. Jawabin da aka saki da sunan ma’aikatar karya ne domin bai fito daga ministan ba.

“Ana shawartan iyaye, dalibai da al’umma da su yi watsi da labaran karyan da aka saki,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani

A wani labarin kuma, mun ji cewa ma’aikatar lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya ta bayyana cewa mutane su shirya gudanar da Sallar Tarawihi a gidajensu saboda ba za'a bude Masallatai ba.

Sallar Tarawihi wacce aka fi sani da Sallar Asham wasu raka’o’i ne da ake gudanarwa bayan Sallan Isha’i a cikin watar Ramadana.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ce sam ba zata daga dokar rufe Masallatai ba sai cutar Coronavirus ta kare gaba daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng