An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani

An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani

- Gwamnatin jahar Kano ta yi feshin magani a wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a jahar

- Kwamishinan Muhalli na jahar, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya jagoranci ma'aikatansa wurin yin feshin

- An dai yi feshin ne a wurare biyar da aka tabbatar ya ziyarta kafin a gane yana dauke da cutar

Gwamnatin jahar Kano ta yi feshin magani a wurare biyar da mutumin da aka tabbatar yana dauke da coronavirus ya ziyarta kafin a gano yana dauke da cutar.

Kwamishinan Muhalli na jahar, Dr Kabiru Ibrahim Getso ne ya jagoranci ma'aikatansa wurin yin feshin, shashin Hausa na BBC ta ruwaito.

An tattaro cewa an yi feshin ne a Masallacin Juma'a na Da’awah da Masallacin Juma'a na Dan Adalan Kano da cibiyar gwajin cututtuka ta Providian Diagonistic.

Sauran wuraren da aka yi feshin sun hada da cibiyar FAN Diagonistic, da asibitin Prime Specialist da kuma gidan mutumin.

An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
Asali: Twitter

Kwamishinan ya jadadda cewar an kulle dukkan wuraren, sannan kuma cewa gwamnati za ta ci gaba da yi musu feshi.

An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
Asali: Twitter

Ku tuna cewa a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, ne aka sanar da batun samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jahar Kano.

An dai rahoto cewa mutumin, wanda ke zaune a karamar hukumar Tarauni, ya baro Abuja inda ya isa Kano a jajiberen ranar da za a rufe hanyoyin shiga jihar.

An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Wata mahaifiyar ‘yan hudu ta mutu bayan ta kamu da cutar

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta rufe wasu daga cikin kasuwannin da ke jihar tare da tsananta dokar hana shiga da fice a kan iyakokinta.

Hakan kuwa ya faru ne sakamakon bullar muguwar cutar coronavirus a jihar a ranar Asabar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya shaidawa BBC cewa tuni aka killace wanda aka samu da cutar a asibitin Pfizer na kwanar Dawaki.

Dan shekaru 75 din da haihuwa na nan a killace don hana yaduwar cutar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel