Rashin Imani: Miyagu sun amshi kudin fansa N4.5m, sa’annan suka kashe yaro dan shekara 15

Rashin Imani: Miyagu sun amshi kudin fansa N4.5m, sa’annan suka kashe yaro dan shekara 15

Wasu miyagu sun yi garkuwa da wani karamin yaro dan shekara 15 mai suna Abubakar Sadiq a jahar Bauchi, inda daga bisani suka halaka shi bayan amsan kudin fansa naira miliyan 4.5.

Premium Times ta ruwaito mahaifinsa, Rilwanu Abubakar, wanda likita ne a asibitin koyarwa ta jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ya bayyana a kofar gidansu aka yi awon gaba da Abubakar.

KU KARANTA: Covid-19: 'Yan sanda sun kama manyan jami'an gwamnati da suka karya dokar hana taro

Rashin Imani: Miyagu sun amshi kudin fansa N4.5m, sa’annan suka kashe yaro dan shekara 15

Rashin Imani: Miyagu sun amshi kudin fansa N4.5m, sa’annan suka kashe yaro dan shekara 15
Source: Facebook

Rilwanu ya bayyana cewa yana wajen aiki aka sanar da shi aukuwar lamarin, nan da nan kuma ya sanar da ofishin yan kato da gora dake yankinsu , da rundunar Yansandan Bauchi.

“Bayan miyagun sun tuntubemu, mun yi yarjejeniya a kan zan basu naira miiyan 3, amma bayan na basu, sai suka nemi mu kara musu, haka suka yi ta neman kari har sai da suka amshi naira miliyan 4.5, sun nemi kari, amma na yi tirjiya.

“Hannu da hannu na basu naira miliyan 2, sai kuma na saka musu N2.5m a asusun bankuna daban daban guda biyar, amma suka cigaba da neman kari, daga nan na yi tirjiya, ashe ma zasu kashe shi.” Inji shi.

Daga bisani an gano gawar Abubakar a wani kango dake kusa da gidansu dake kan titin Gombe a garin Ningi, inda aka yi masa jana’iza, sa’annan aka binne shi kamar yadda addini ya tanada.

Sai dai Dakta Rilwanu ya yi zargi miyagun da suka aikata hakan sun san shi tare da iyalansa kwarai da gaske duba da yadda suka sace shi da kuma inda suka binne gawarsa.

Rundunar Yansandan Bauchi ta bakin Kaakakinta, Kamal Datti ta tabbatar da labarin, inda ta ce an gano gawar yaron, kuma sun kama mutane 2 da suke zarginsu da hannu a lamarin.

A wani labarin kuma, Yayan gwamnan jahar Bauchi, Yaya Adamu ya kubuta daga hannun miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan kwashe kwanaki 12 a hannunsu.

Kaakakin Yansandan jahar, ya bayyana haka ga manema labaru a daren Talata, 7 ga watan Afrilu. Sai dai bai bayyana ko an biya kudin fansa kafina sako Yaya Adamu ba, ko kuwa a’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel