Hana fita da taron jama'a: An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja
Kwamitin tabbatar da biyayya ga umarnin zama a gida da hana taron jama'a a Abuja ya kama wani shugaban al'ummar Musulmi da ya sabawa matakin da hukuma ta dauka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.
Shugaban kwamitin, Ikharo Attah, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.
Ya kara da cewa, jami'an kwamitinsa sun kwace motoci 269 bayan samunsu da laifin sabawa umarnin a zauna a gida.
"Mun fara aiki da sanyin safiyar yau (Lahadi) bayan wasu 'yan kasa nagari sun kiramu tare da sanar da mu cewa za a yi taron ibada a wata coci da ke unguwar Durumi.
"Bayan mun isa Cocin sai muka iske cewa hakan ba gaskiya bane, amma mun sami Fasto a cikin Cocin tare da masu daukan hoton bidiyo.
"Daga nan sai muka wuce zuwa wani Masallaci da aka tabbatar mana da cewa babban Limamin Masallacin ya jagoranci jama'a sallar Juma'a a yankin Wuye," a cewar Attah.
Ya gargadi jama'a, musamman wadanda ba aikin tsaro suke ba, a kan karya doka.
A wani labarin mai nasaba da wannan, Legit.ng ta wallafa cewa 'yan sanda a jihar Nasarawa sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar da suka karya dokar da gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya kafa a kan killace kai tare da hana taron jama'a saboda dakile yaduwar annobar cutar covid-19.
DUBA WANNAN: Covid-19: Mutane uku sun kara mutuwa a Najeriya, annobar ta shiga jihohi 20
Manyan jami'an gwamnatin da aka kama sune; Alhaji Suleman Agyo, shugaban karamar hukumar Lafiya ta kudu da Mukhtar Wakeel, mukaddashin rijistara a kwalejin kimiyya da fasaha da ke garin Lafiya.
Faifan bidiyon bikin auren shugaban karamar hukumar ya yadu a dandalin sada zumunta, musamman a tsakanin mazauna garin Lafiya.
Da ya ke tabbatar da kama manyan jami'an gwamnatin a ranar Lahadi, kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Bola Longe, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin sabawa umarnin gwamnatin jiha.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng