Hukumar LASUTH ta killace Ungonzoman da su ka kula da Mai cutar COVID-19

Hukumar LASUTH ta killace Ungonzoman da su ka kula da Mai cutar COVID-19

Asibitin koyon aiki na Jami’ar jihar Legas watau LASUTH ta ce ta killace wasu Ma’aikatanta bayan sun yi hulda da Mata da mutu a sanadiyyar annobar cutar nan ta COVID-19.

Shugaban asibitin LASUTH, Tokunboh Fabamwo, ya shaidawa hukumar dillacin labarai na kasa wannan mataki da su ka dauka a lokacin da ya zanta da su a cikin karshen makon nan.

Hukumar NAN ta rahoto Farfesa Tokunboh Fabamwo ya na cewa wannan ba bakon abu ba ne wajen aikinsu ganin yadda wata Maras lafiya ya mutu wajen jinya a asibitin kwanaki.

Farfesa Fabamwo ya ce“Duka Likitocinmu sun dauki matakan kare kai a lokacin da su ke kula da Maras lafiyar. A lokacin da Matar ta ke daf da mutuwa, ta na numfashi da kyar, Unguzomomi sun ruga wajen ta domin yunkurin ceto rayuwarta.”

Sun matsa kusa da ita, duk da su na da kariya, mu na ganin cewa saboda kusancin da su ka samu, ya kamata mu kebe su daga Jama’a, saboda haka ba za su koma gida su jefa Iyalansu cikin hadari ba.”

KU KARANTA: An sallami Firayim Ministan Birtaniya bayan ya murmure daga COVID-19

Shugaban asibitin ya bayyana cewa tuni Likitoci sun dauki jinin Marigayiyar da na Mai dakinta domin ayi masu gwaji. Yanzu ana jiran sakamakon gwajin mijin.

Fabamwo ya kara da cewa za a dauki tsauraran matakai na kare jama’a daga kamuwa da wannan cuta. Daga cikin matakan shi ne za a rika auna zafin jikin masu zuwa asibitin ziyara.

Rahoton ya bayyana cewa wannan Mata da ta mutu ta na fama da wata rashin lafiya kafin a kawo ta asibitin LASUTH. Bayan ‘yan kwanaki kadan ta na jinya, ta ce ga garin ku nan.

Kawo yanzu akwai mutane fiye da 300 da su ka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya. Daga cikinsu akwai fiye da 170 a Legas. Mutane 70 ne su ka warke yayin da cutar ta kashe mutane 10.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng