COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a

COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a

- Wanda aka gano yana dauke da cutar coronavirus a jihar Kano ya ziyarci a kalla wurare uku kuma akwai yuwuwar ya shafa wa wasu cutar

- An gano cewa mutumin ya je masallacin Juma'a, ya ziyarci wani asibitin kudi da kuma kwatas din da gidan shi yake

- A ranar 11 ga watan Afirilun 2020 ne jihar Kano ta samu mutum daya da ke dauke da cutar coronavirus

Mutumin da ke dauke da cutar coronavirus a jihar Kano ya je sallar Juma'a a Masallaci, rahoton aridar Daily Trust ya bayyana.

Wannan lamarin kuwa ya jawo rudani da tsananin tashin hankali ga manyan jami'an gwamnatin jihar.

Idan zamu tuna, jihar Kano ta samu mutum na farko mai dauke da cutar a ranar Asabar, 12 ga watan Afirilu.

An gano cewa an kwantar da mutumin ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke GRA Nasarawa a jihar Kano.

Wata majiya daga asibitin ta bayyana cewa, an kwashe dukkan ma'aikata da majinyatan asibitin inda aka killacesu.

COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a
COVID-19: Rudani a Kano bayan an gano mai coronavirus ya halarci sallar Juma'a
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shugaban kasar Chadi ya caccaki gwamnatin Najeriya a kan sakin 'yan Boko Haram (Bidiyo)

An gano cewa, an kara da kwashe wasu masu makwabtaka da asibitin don gwaji.

Majinyacin dai yana da shekaru 75 kuma tsohon jakada ne. Ya isa Kano ne daga Legas, inda ake zargin ya debo cutar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, an hana kanwarsa shiga gidan iyalan mutumin.

Hadiman gidan tare da iyalansa da ke kwatas din Giginyu duk an kwash su zuwa cibiyar killacewa.

Hankalin jama'a mazauna wurin ya matukar tashi bayan gano wa da aka yi cewa mutumin na dauke da cutar.

Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, kwamishinan lafiya na jihar Kano, ya ce an tura jami'an kwamitin hana yaduwar cutar zuwa wurare uku da mutumin ya je.

Wuraren da ya ziyarta kuwa sun hada da kwatas din Giginyu, masallacin Juma'a na Da'awah da kuma asibitin kudin da aka kwantar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel