Mun kafa wuraren gwajin COVID-19 a asibitocin Kano da Filato - Hukumar NCDC

Mun kafa wuraren gwajin COVID-19 a asibitocin Kano da Filato - Hukumar NCDC

Hukumar NCDC mai yunkurin takaita yaduwar cututtuka a Najeriya ta na cigaba da kokarin ganin bayan annobar Coronavirus da ta barkowa kasar da sauran kasashen Duniya.

A dalilin haka ne hukumar NCDC ta tashi tsayin daka wajen samar da wuraren yin gwajin wannan cuta ta COVID-19. Kafin yanzu babu dakin wannan gwaji a kaf jihohin Arewa.

A halin yanzu hukumar ta tabbatar da cewa ta kirkiri sababbin dakunan gwajin COVID-19 a wasu manyan asibitoci da ke jihar Kano da kuma jihar Filato duk a Yankin Arewacin Najeriya.

A Ranar Juma’a kun samu labarin dakin gwajin da aka kafa a jihar Kano. NCDC ta kirkiri wannan dakin gwaji ne a asibitin koyar da aikin Likitanci na Malam Aminu Kano da ke Jihar.

An kafa wannan dakin gwaji ne a sashen binciken cutar sanyi da ke wannan asibiti kamar yadda mu ka samu labari. Wannan shi ne dakin gwajin farko da aka yi a Arewa maso Yamma.

KU KARANTA: An fara binciken magungunan da za su warkar da COVID-19

Haka zalika a jihar Filato, hukumar NCDC ta bayyana cewa ta kafa wannan dakin gwaji na kwayar cutar COVID-19 ne a cibiyar binciken ciwon dabbobi da ke Garin Vom a jihar.

NCDC ta tabbatar da wannan a wani bayani da ta yi a shafinta na sada zumunta na Tuwita. Hukumar ta fitar da wannan gajeren bayani ne a jiya Ranar 11 ga Watan Afrilun, 2020.

Da wannan kokari da hukumar ta yi, ya zama ana da dakunan gwajin COVID-10 har 11 a Najeriya. Daga ciki akwai uku a jihar Legas sai kuma biyu a babban birnin tarayya da ke Abuja.

Haka zalika akwai dakunan gwajin a jihohin Oyo, Osun, Ebonyi da kuma Edo. Sai kuma yanzu da aka bude sababbi a Kano da Filato da za su taimaka wajen iya yin gwajin a Arewa.

Hukumar ta bayyana cewa yanzu ta na kokarin kafa wasu sababbin dakunan gwajin a Birane hudu. Wadannan Garuruwa ne su ne Maiduguri, Sokoto, Fatakwal da kuma Kaduna

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel