Jerin Jihohin Najeriya da har yanzu ba a samu bullar COVID-19 ba

Jerin Jihohin Najeriya da har yanzu ba a samu bullar COVID-19 ba

Daga lokacin da aka fara samun wanda ya fara kamuwa da COVID-19 a Najeriya a karshen Watan Junairun bana zuwa yanzu, fiye da mutane 300 cutar ta kama kawo yanzu.

Kamar yadda mu ka samu rahoto daga alkaluman da hukumar NCDC mai yunkurin takaita yaduwar cututtuka a Najeriya ta fitar, annobar ta shiga jihohi 19 da birnin tarayya.

A wani bangare guda kuma jihohin da aka samu bullar cutar su ne: Osun Oyo, Ogun, Bauchi, Kaduna, Akwa – Ibom, Katsina, Delta, Enugu, Ribas, Ondo da kuma jihar Kwara.

Ragowar jihohin su ne Benuwai, Neja, Anambra sai kuma Kano da cutar ta bulla a karshen makon nan. Haka kuma akwai mutane 56 da su ka kamu da cutar a birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa mun kawo jerin jihohin da wannan cuta ba ta shiga ba tukuna.

1. Abia

2. Adamawa

3. Bayelsa

4. Borno

5. Kuros Riba

6. Ebonyi

7. Gombe

8. Imo

9. Jigawa

10. Kebbi

11. Kogi

12. Nasarawa

13. Filato

14. Sokoto

15. Taraba

16. Yobe

17. Zamfara

KU KARANTA: 10 daga cikin mutum 100, 000 da COVID-19 ta kashe su na Najeriya

Idan aka lura za a fahimci cewa daga cikin wadannan Jihohi da aka ambata, 12 su na Yankin Arewacin kasar ne, yayin da ragowar biyar su ka fito daga Kudancin kasar.

Jihohin Kudun su ne Abia, Bayelsa, Kuros Riba, Ebonyi da Imo. Abin da hakan ya ke nufi shi ne babu jihar Kudu maso Yammacin kasar nan da wannan cuta ba ta shiga ba.

Yankin Arewa maso Gabas ne ya fi kowane Yanki tsira daga cutar a yanzu, a kaf wannan Yanki a jihar Bauchi ce kadai wannan cuta ta bulla, har mutane shida su ka kamu da ita.

A Arewa maso Yamma ba a samu bullar cutar a Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jigawa ba. Kawo yanzu babu wanda ya kamu da cutar a Arewa ta tsakiya daga Kogi, Nasarawa da Filato.

A zuwa Ranar Asabar, 11 ga Watan Afrilun 2020 da dare, mutane 318 su ka kamu da cutar daga cikin jihohin Najeriya 19. An samu mutane 70 da su ka warke, inda 10 su ka mutu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel