Dokar hana walwala: An damke dan sanda ya karba cin hancin N40,000

Dokar hana walwala: An damke dan sanda ya karba cin hancin N40,000

- Wani dan sanda da ke aiki a Okota da ke Oshodi, karamar hukumar Isolo da ke jihar Legas ya shiga hannun hukuma bayan an gano ya karba cin hanci daga wani mai abun hawa

- Ana zargin mai abun hawan da karya dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka don hana yaduwar muguwar cutar coronavirus a cibiyar kasuwancin kasar nan

- Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya sanar da wakilin jaridar The Punch cewa sun kama dan sandan

Wani dan sanda da ke aiki a Okota da ke Oshodi, karamar hukumar Isolo da ke jihar Legas ya shiga hannun hukuma bayan an gano ya karba cin hanci daga masu ababen hawa.

An ga wani dan sanda mai matsayin sifeta mai suna Taloju Martins yana kirga takardun dubu daddaya har guda arba'in a wani bidiyo.

Kudin dai tamkar na fansa ne wanda wani mai abun hawa ya bashi don ya sakar masa abun hawansa.

Ya zargin mai abun hawan da karya dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka don hana yaduwar muguwar cutar coronavirus a jihar ta Legas.

Dan sandan ya bukaci mai abun hawan da aka kwacewa mota da ya biya N50,000 amma sai ya roka aka bar mishi a N40,000.

Dokar hana walwala: An damke dan sandan ya karba cin hancin N40,000
Dokar hana walwala: An damke dan sandan ya karba cin hancin N40,000
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

Amma kuma a rashin sanin Martins, mai motar ya nadi bidiyonsa a yayin da suke yin wannan cinikin.

Kamar yadda bidiyon da mawaki mai suna Rugged Baba ya wallafa, ya ce lamarin ya faru a ranar Juma'a ne, 10 ga watan Afirilu a titin fadar Ago da ke Okota.

Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya sanar da wakilin jaridar The Punch cewa sun kama dan sandan.

Ya kara da cewa dan sandan mai mukamin sifetan zai fuskanci ladabtarwa kamar yadda dokokin hukumar 'yan sandan ta tanadar.

"Mun ga bidiyon kuma mun damke sifetan. Mun fara bincike kuma zai fuskanci ladabtarwa kamar yadda hukumar 'yan sandan ta tanadar," Elkana ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel