Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisa Shija ya bar PDP, akwai yiwuwar komawarsa APC

Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisa Shija ya bar PDP, akwai yiwuwar komawarsa APC

- Tsohon dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Farfesa Terhemba Shija ya sanar da cewa ya bar jam'iyyar kwata-kwata

- Tsohon dan majalisar tarayyar ya sanar da barin jam'iyyar da ya kwashe shekaru sama da 20, a wata wasika mai kwanan wata 8 ga Afirulu

- Kamar yadda bincike ya bayyana, akwai yuwuwar kusancin farfesan da Gwamna Akume ne ya jawo barin jam'iyyar

Tsohon dan siyasa a jam'iyyar PDP, Farfesa Terhemba Shija ya sanar da barin jam'iyyar.

Farfesa Shija ya kasance a PDP ne tun a shekarar 1999 inda ya kasance jigo.

A wata wasika mai kwanan watan 8 ga Afirilun 2020, wacce aka mika ga shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Vandeikya, Farfesan yace ya fita daga jam'iyyar ne saboda dalilan kansa.

Ya kara da bayyana cewa ya dauka shekaru 20 ko fiye da hakan yana bautawa jam'iyyar. Yanzu lokaci yayi da zai kara gaba don cimma wasu burikan rayuwarsa wadanda yace PDP ba za ta iya samar masa ba.

A yayin da yake fatan alheri ga jam'iyyar, Shija yace ba ya rike da wani mugun nufi ga jam'iyyar ko 'ya'yanta.

Amma kuma jaridar The Nation ta gano cewa, farfesan turancin kuma tsohon dan majalisar tarayyar zai iya garzayawa jam'iyyar APC.

Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisa Shija ya bar PDP, akwai yiwuwar komawarsa APC
Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisa Shija ya bar PDP, akwai yiwuwar komawarsa APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

Shija ya yi aiki da shugaban jam'iyyar APC na jihar Benue, Gwamna George Akume.

Shija sannanen gogaggen dan siyasa ne wanda mutane da yawa ke masa hangen takarar gwamnan jiharsa a 2023 karkashin jam'iyyar APC.

Jaridar The Nation ta gano cewa, akwai yuwuwar Sanata Akume ne ya jawo hankalin Shija da ya dawo APC don ya samu tikitin takarar gwamnan jihar.

Tun bayan da ya sanar da barin PDP, gidansa da ke titin Gboko ya zama tamkar wajen sauke farali ga manyan 'yan siyasa da kungiyoyi daban-daban.

Manyan 'yan siyasa na ta kaiwa da kawowa a gidansa don jawo ra'ayinsa zuwa jam'iyyunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel