Coronavirus ta kashe mutum 2,000 a Amurka a rana daya

Coronavirus ta kashe mutum 2,000 a Amurka a rana daya

Kasar Amurka ce kasa ta farko da ta sanar da mutuwar fiye da mutane 2,000 da suka kamu da coronavirus a rana daya a yayin da galibin sauran kasashen duniya ke hutun Easter a killace a gidansu.

Jimillar wadanda annobar ta kashe a duniya ya tasanma 103,000 a ranar Jumaa, inda Amurka ce ke da adadin da ya fi kowa a yanzu bayan bullar cutar a China kamar yadda The unch ta ruwaito.

Kawo yanzu dai adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar sun fi yawa ne a kasashen Turai duk da cewa an fara samun saukin yaduwar ta a wasu kasashen.

A Faransa, an samu kimanin mutane 1,000 da suka mutu a ranar Jumaa amma an ruwaito cewa adadin wadanda cutar ya yi wa illa sosai suna raguwa.

Coronavirus ta kashe mutum 2,OOO a Amurka a rana daya

Coronavirus ta kashe mutum 2,OOO a Amurka a rana daya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Masana kimiyya sun gano magunguna 6 da ka iya kashe coronavirus

A kasar Italy ta ce adadin wadanda suke mutuwa a kowane rana yana raguwa duk da cewa gwamnatin ba ta amince ta dage dokar tilasta wa alumma zaman gida da ta saka ba har sai ranar 3 ga watan Maris.

Italy ce ka kan gaba wurin adadin wanda cutar ya kashe da suka kai 18,849 amma akwai yiwuwar Amurka za ta kece ta idan har adadin wadanda ke mutuwa a rana ya cigaba yadda ya ke a wannan makon.

A ranar Jumaa, Amurka ta ruwaito cewa mutum 2,108 ne cutar ya kashe, wannan shine adadin da ya fi yawa a rana guda tun bayan bullar cutar a birnin Wuhan a watan Disamba.

A halin yanzu Amurka ce ka da mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya inda ta ruwaito cewa wadanda suka kamu sun fi 500,000 .

Adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya a yanzu ya dara miliyan 1.7 duk da cewa wasu kasashen kawai su na yi wa wadanda suka fara nuna alamun cutar ne gwaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel