Kalu, Dariye, Nyame, Metuh basu cikin fursunonin da Buhari ya yafewa - Hukumar gidajen gyara hali

Kalu, Dariye, Nyame, Metuh basu cikin fursunonin da Buhari ya yafewa - Hukumar gidajen gyara hali

Kakakin hukumar gidajen gyara halin Najeriya, Chuks Njoku, ya bayyana cewa tsaffin gwamnonin aka jefa gidan yari kan laifin rashawa da almundahana basu cikin wadanda za'a saki.

Za ku tuna cewa shugaba Buhari ya yafewa fursunoni 2600 kuma ya bada umurnin sakesu.

Chuks Njoku ya yi watsi da rahotannin cewa da yiwuwan a saki manyan yan siyasan dake cikin gidajen yari saboda yawan shekarunsu.

Ya ce adadin shekarun gwamnonin dake yawo a kafafen sadarwa ya sabawa wanda ke hannun hukumar.

Njoku yace: "Muna da sharrudanmu kuma basu cancanci afuwar ba. Basu cika ko daya cikin sharrudan da aka kindaya ba."

"Idan an kama ka da laifi, sai ka zauna na wasu yan shekaru kuma ka gyara halin ka tare da nuna nadamar abinda kayi a baya."

"Ba maganan yawan shekarun mutum bane; akwai da dama cikinsu da sun tsufa amma basu cancanta ba. Saboda haka wadanda zasu amfana sai sun kwashe wasu yan shekaru kuma ya kasance ba babban laifi suka aikata ba."

"Tsaffin gwamnonin basu cancanta ba saboda basu dade da zuwa (gidan yari) ba kuma har yanzu wasu na kotun daukaka kara."

Kalu, Dariye, Nyame, Metuh basu cikin fursunonin da Buhari ya yafewa - Hukumar gidajen gyara hali

Hukumar gidajen gyara hali
Source: Facebook

Za ku tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin sakin yan gidan yari 2,600 a fadin tarayya domin rage cinkoso cikin gidajen gyara halin Najeriya.

Shugaban kasan ya bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya wajen yafewa fursunonin domin rage yawansu a gidajen yari saboda cutar Coronavirus.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya fadin hakan a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu, 2020 a hira da yayi da manema labarai.

A cewarsa, za a saki fursuna 70 daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranarAlhamis, sannan daga baya a saki fursunonin dake gidajen yarin sauran jihohi irinsu Kiri-kiri Dss.

Ga jerin fursunonin da aka yafewa

1. Tsofaffi masu shekaru akalla 60

2. Masu fama da rashin lafiya mai tsanani

3. Fursunonin da wa'adinsu da ya rage na kasa da watanni shida

4. Masu ciwon tabin hankali

5 Wadanda aka ci tarar su kasa da N50,000.

Amma ya bayyana cewa ba za a saki wadanda aka kama da laifin ta'addanci, satar mutane da kisan kai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel