Muhimman abubuwa 2 da muka tattauna da shugaban kasa - Osinbajo

Muhimman abubuwa 2 da muka tattauna da shugaban kasa - Osinbajo

- A ranar Juma'a da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sadu da mataimakinsa, Yemi Osinbajo

- Shugaban kasa Buhari ya umarci mataimakinsa da ya shugabanci sabon kwamitin daidaita tattalin arziki da aka kafa

- Shugaban kasar da mataimakinsa sun yi amfani da taron ne wajen tattaunawa a kan matsalolin matalauta da kuma yadda za a datse yaduwar annobar

A ranar Juma'a da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sadu da mataimakinsa, Yemi Osinbajo don tattauna hanyoyin hana yaduwar cutar coronavirus.

Hakazalika, shugaban kasar da mataimakinsa sun tattauna yadda tattalin arzikin kasar nan zai daidaita.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci mataimakinsa da ya shugabanci sabon kwamitin daidaita tattalin arziki da aka kafa.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasar a gidan gwamnati da ke Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan.

Ya ce tattaunawar sun yi ta ne a kan manyan matsalolin kasar nan na annoba da tattalin arziki.

Muhimman abubuwa 2 da muka tattauna da shugaban kasa - Osinbajo
Muhimman abubuwa 2 da muka tattauna da shugaban kasa - Osinbajo
Asali: UGC

KU KARANTA: Kisan dakarun Chadi: Buhari ya yi alkawarin daukar tsauraran matakai a kan Boko Haram

Shugaban kasar da mataimakinsa sun yi amfani da taron ne wajen tattaunawa a kan matsalolin matalauta da kuma yadda za a datse yaduwar annobar coronavirus a kasar nan.

Osinbajo ya ce: "Na zo bayani ne ga shugaban kasa kamar yadda na saba. Wasu lokutan na kan zo da kaina kamar yau, wasu lokutan kuwa ta waya nake mishi bayani.

"Abinda muke son tabbatar wa shine daidaituwar tattalin arziki, kare ayyukan jama'a da samar da karin ayyukan ga jama'ar kasar nan.

"Shugaban kasar ya nuna matukar damuwar shi a kan matsalolin da ke tattare da wannan kullen da aka yi wa 'yan kasa. Mutane da yawa na fita neman abinda za su ci a kullum.

"Don haka dole ne mu san yadda za mu yi da su a wannan lokacin. Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da muka tattaunawa kuma masu amfani ga kasar nan", yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel