Bamu kammala tattaunawa kan lamarin bada wuta kyauta ba - FG ga yan Najeriya

Bamu kammala tattaunawa kan lamarin bada wuta kyauta ba - FG ga yan Najeriya

Ministan wutan lantarki, Saleh Mamman, ya ce basu kammala tattaunawa da kamfanonin da ke rarraba wuta lantarki ba kan lamarin baiwa yan Najeriya wuta kyauta na tsawon wanni biyu.

Hakan ya biyo bayan jawabin kungiyar kamfanonin raba wutar lantarki a Najeriya (DisCos) inda suka ce gwamnatin tarayya zata biya kudin wutan da ake shirn baiwa jama'a kyauta.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a inda yace idan gwamnati ta kammala tattaunawa, za a sanarwa yan Najeriya.

Ministan ya tabbatarwa yan Najerya cewa gwamnati na iyakan kokarinta wajen yaye halin radadin da annobar Coronavirus ta daurawa kasa.

Yace “Gwamnatin tarayya bata yanke shawara kan cewa za a baiwa yan Najeriya wutan lantarki kyauta na tsawon watanni biyu ba.“

“Idan mukayi hakan, za a sanar a hukumance.“

“Ina baku tabbacin cewa gwamnatin tarayya na neman hanyoyin da zata yayewa yan Najeriya wahala.“

KU KARANTA An sake sallaman mutane 7 bayan sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

Bamu kammala tattaunawa kan lamarin bada wuta kyauta ba - FG ga yan Najeriya
Saleh mamman
Asali: Twitter

KU KARANTA An sake sallaman mutane 7 bayan sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

A wani labarin daban, Wata kungiya mai suna The Concerned Citizens of Zamfara State ta bayyana cewa akwai yiwuwar jamiyyar APC ta rasa mambobi da magoya bayan ta masu yawa idan Gwamna Bello Matawalle ya shiga jamiyyar.

A cewar kungiyar, shigar gwamnan jamiyyar babban kuskure ne a siyasance inda ta yi ikirarin ba shi da cancanta da zai jagoranci mutane a harkar siyasa.

Sun yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan rahoton cewa wasu manyan APC suna yi wa gwamnan matsin lamba cewa ya shigo jamiyyar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren kungiyar, Comrade Musa Gusau, ya ce mafi yawancin wadanda ke yi wa Matawalle matsin lamba ya shiga APC yan PDP ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel