Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 7 bayan sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 7 bayan sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa an kara sallamar mutane biyar daga asibitin jinyar masu cututtuka IDO dake unguwar Yaba ta jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Juma'a, 10 ga Afrilu, 2020.

Ya ce: “Yau, An sallami mutane bakwai wanda ya hada da maza 4 da mata 3 bayan an tabbatar da sun warke daga cutar COVID-19 bayan gwaji biyu daban-daban, kuma tuni an hadasu da iyalansu. “

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 7 bayan sun warke daga cutar Coronavirus a Legas

Coronavirus a Legas
Source: Depositphotos

KU KARANTA An samu karin masu cutar Coronavirus 16, Jimilla 305

Duk a yau, mutane uku ne suka warke daga cutar coronavirus a jihar Oyo, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

An sallamesu daga cibiyar killace masu fama da cututtuka masu yaduwa bayan an gane sun warke sarai.

An damka su ga 'yan uwansu bayan gwaji kashi na biyu ya nuna sun warke daga cutar. Wannan ne yasa jimillar wadanda aka sallama masu cutar a jihar suka kai biyar.

Sauran shida ne ke asibiti suna jinya.

Gwamna Seyi Makinde, wanda ya ke jagorantar kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Oyo, ya bayyana hakan ne yayin jawabi a kan kokarinsu na fatattakar cutar.

Amma kuma, Gwamnan ya sake jaddada haramcin taron sama da mutane 10 a jihar. Ya ce dokar ta-bacin da aka saka a jihar har yanzu ba a dage ta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel