COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan ya killace kansa

- Firgici da fargaba sun shiga zukatan jama'ar jihar Kano a kan mutuwar wani bawan Allah mazaunin kwatas din Gwammaja

- Kamar yadda makwabtan Abdulrasheed Ibrahim suka bayyana, ya dawo Kano ne daga Abuja a ranar Litinin da ta gabata

- Makwabtansa sun bayyana cewa sun ganshi yana wanke motarsa a ranar da ya dawo, kafin ya killace kansa

Firgici da fargaba ta shiga zukatan jama'ar jihar Kano a kan mutuwar wani Abdulrasheed Ibrahim.

Mazaunin kwatas din Gwammajan ya mutu ne bayan ya killace kansa.

Kamar yadda makwabtan mamacin suka bayyana, marigayi Abdulrasheed ya dawo Kano ne daga Abuja a ranar Litinin da ta gabata, jaridar The Nation ta ruwaito.

Makwabtansa sun bayyana cewa sun ganshi yana wanke motarsa a ranar da ya dawo, kafin ya killace kansa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mazaunan yankin sun dinga jin wani wari na fitowa daga gidan mamacin.

Sun lura kuma yana cikin gida baya fitowa har na tsawon kwanaki uku.

COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan an killace shi
COVID-19: Wani mutum ya mutu a Kano bayan an killace shi
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Coronavirus: Fitattun 'yan Najeriya 6 da suka warke daga COVID-19 (Hotuna)

Wadannan dalilan ne suka sa mazauna yankin suka sanar da 'yan uwan shi wadanda suka balle gidan tare da samunsa a mace.

Kokarin zantawa da 'yan uwan mamacin ya gagara a halin yanzu.

Daraktan cibiyar kula da lafiyar jama'a da hana yaduwar cutuka na jihar, Dr Imam Wada Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu don jami'an kiwon lafiya sun isa wurin don daukar matakan da suka dace.

Kamar yadda yace, an dau samfurin jinin mamacin kuma za a gwada. Ya tabbatar wa da jama'a cewa za a sanar musu sakamakon gwajin.

A wani labari na daban, cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta kammala kafa cibiyar gwajin cutar Coronavirus a asibitin koyarwar Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.

Kafa wannan cibiyar cika alkawari ne da gwamnatin tarayya tayi na samar da dakin bincike na musamman domin gwajin cutar COVID-19 a Kano da wasu jihohin Arewa maso yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel