Coronavirus: Fitattun 'yan Najeriya 6 da suka warke daga COVID-19 (Hotuna)
A yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2020, an samu mutane 288 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 a Najeriya kamar yadda Hukumar Kula da Cututtuka masu Yaduwa, NCDC, ta tabbatar.
Daga cikin mutane 288 da suka kamu da cutar, mutane 51 sun warke yayin da mutane bakwai ne suka rasu.
Legit.ng ta gano cewa cikin wadanda suka warke daga cutar akwai wasu fitattun yan Najeriya guda shida kamar haka
1. Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi yana daga cikin wadanda suka warke daga cutar.
An yi masa gwaji har sau biyu an kuma gano cewa babu sauran kwayar cutar a jikinsa.
Ya sanar da warkerwarsa a Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Afrilu inda ya mika godiyarsa ga Allah da shugabanin addini da suka masa addua da kuma tawagar NCDC.

Asali: Twitter
2. Seyi Makinde
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya kamu da COVID-19 amma ya warke. An masa gwajin sau biyu cikin mako guda duk kuma sakamakon ya nuna ya warke.
Makinde ya ce ya yi amfani da karas, Vitamin C, habbatus sauda da zuma wurin yaki da kwayar cutar.

Asali: Twitter
Sai dai hukumar ta NCDC ta ce kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar suna warkewa ba tare da wani magani na musamman ba inda ta ce har yanzu cutar ba ta da magani.
3. Farfesa Jesse Otegbayo
Shugaban asibitin koyarwa ta Jamiar Ibadan, UCH, Farfesa Jesse Otegbayo shima ya kamu da COVID-19.
Kamar Gwamna Makinde, shima ya warke daga muguwar cutar.
A ranar Laraba 8 ga watan Afrilu, shugaban asibitin ya yi bayanin irin halin da ya shiga yayin da ya kamu da cutar amma imanin da ya yi da Allah ya taimaka masa.

Asali: UGC
4. Oluwaseun Ayodeji Osowobi
A Disambar 2O19, Oluwaseun Ayodeji Osowobi, an karrama wacce ta kafa kungiyar yaki da fyade ta Stand to End Rae Initiative, STER, da lambar yabo na 'Commonwealth Young Person of the Year Award' ta shekarar 2019 saboda ayyukan da ta yi.
An bawa wasu zababun matasa irin wannan lambar yabon daga nahiyoyin Asia, Afirka, Turai, Amurka da sauransu tare da kyautan kudi Naira Biliyan 2.3

Asali: Twitter
Matashiyar ta tafi Birtaniya inda ta hallarci taron hadin kan kasashen da Birtaniya ta raina a kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.
Daga bisani ta kamu da cutar an kuma killace ta a Legas na wasu makonni sannan aka sallamo ta bayan ta warke.
5. Salihu Umar
Salihu Umar ba wani sananne bane a baya amma ya yi fice bayan ya fito a Twitter ya sanar da duniya cewa ya kamu da kwayar cutar kuma bai damu da duk wani tsangwama da za a iya masa ba.
Ya kwashe makonni a wurin killace wa a babban birnin tarayya Abuja kuma daga baya ya warke daga cutar.
6. Seun O
Seun O, fitaccen mai daukan hoto shima ya warke daga cutar. Matashin ya bayyana warkewarsa a shafin sada zumunta.
A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Seun ya hallarci taron African Magic Viewer's Choice Award a Birtaniya.
Kwana daya bayan dawowarsa, ya fada wa abokinsa cewa ba shi da lafiya kuma yana zargin coronavirus ne.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng