Rigingimu 5 da ke tsakanin hukumar tace fina-finai da Kannywood

Rigingimu 5 da ke tsakanin hukumar tace fina-finai da Kannywood

Matakin da hukumar tace fina-finai ta Kano ta dauka na dakatar da shirin Kwana Casa'in da kuma Gidan Badamasi ya jawo mata caccaka da yabo daga wajen jama'a.

Ba wannan ne karon farko da hukumar ke fuskantar ce-ce-ku-ce ba daga jama'a sakamakon wasu ayyukanta.

Mutane da yawa kan zargi hukumar da saka siyasa a lamuranta yayin yanke wasu hukunci.

Rigingimu masu tarin yawa sun saba shiga tsakanin hukumar da masana'antar Kannywood. Ga wasu daga cikin rigingimun da suka gibta tsakanin bangarorin biyu:

Sanusi Oscar

A watan Augustan 2019 ne hukumar ta gurfanar da daraktan a kan saba wasu ka'idoji da yayi. An zargi Oscar da bada umarnin wata waka da ta sabawa al'adar Kano, lamarin da mawakin ya ce bai shafe shi ba don ba wakar shi bace.

Naziru Sarkin Waka

A watan Satumba ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta damke Naziru. Hukumar tace fina-finan da ta bada wannan umarnin ta zargesa da laifin mallakar dakin waka a gida.

Amma kuma fitaccen mawakin ya musanta tare da zargar hukumar da taka rawa ga gangar siyasa ne kawai.

Rigingimu 5 da ke tsakanin hukumar tace fina-finai da Kannywood
Rigingimu 5 da ke tsakanin hukumar tace fina-finai da Kannywood
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shari'a za ta yi iyaka tsakanin Arewa24 da hukumar tace fina-finai

Sani Danja

A watan Fabrairun wannan shekarar ne hukumar tace fina-finan ta garkame dakin daukar hoton jarumi Sani Danja.

Hukumar ta ce tayi hakan ne don fitaccen mawakin bai cika sharuddan rijistar dakin daukar hoton ba.

Adam Zango

A watan Fabrairu ne hukumar tace fina-finan ta sha alwashin kwamushe jarumi kuma mawaki Adam A. Zango matukar ya shiga jihar Kano.

Dama can akwai wata jikakkiya tsakanin hukumar da jarumin tun bayan da ya ki rijista da ita. Hakan yasa suka hana shi gudanar da wasa matukar bai yi rijistar ba.

Akwai yuwuwar irin wadannan rigingimun su ci gaba da kunno kai tsakanin hukumar tace fina-finan da masana'antar.

Hakan kuwa zai ci gaba da assasa wutar rigingimun duk da hukumar tace fina-finan ta ce tana yin hakan ne don tsaftace masana'antar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng