2023: Gwamnan Kogi ya yi bayani a kan fastocin kamfen dinsa da ke yawo

2023: Gwamnan Kogi ya yi bayani a kan fastocin kamfen dinsa da ke yawo

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nisanta kanshi da fastocin da ke yawo na yakin neman zabensa na shugabancin kasa

- Gwamnan ya ce bai san kungiya ko mutanen da suka buga fostocin ba a cikin wannan tsaurin rayuwar da duniya ke fuskanta

- Ya ce tunaninsa da hankalin shi duk suna kan jama'ar jihar Kogi ne sakamakon jajircewa da suka yi wajen zabensa

Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya nisanta kansa daga fastocin yakin neman zaben sa a matsayin shugaban kasa a 2023 da ke yawo.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, wata fosta mai dauke da logon jam'iyyar APC tare da kaloli na yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

Kamar yadda yake rubuce a fotocin, "Domin ci gaba da shugabanci na gari, a zabi APC. A zabi Gwamna Yahaya Bello a matsayin shugaban kasar Najeriya".

Amma kuma, takardar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Onogwu Muhammed ya fitar a ranar Alhamis a garin Lokoja, ya ce Bello bashi da masaniya a kan hakan.

Ya kara da cewa bashi da hadi da fastocin, kungiya ko wani mutum da yayi sanadin bayyanarsu.

Muhammed ya ce, "Hankalin gwamnan ya kai ga wasu hotuna da fastoci da aka shirya da hotonsa wadanda ke bayyana yakin neman zabensa a matsayin shugaban kasa a 2023".

2023: Gwamnan Kogi ya yi bayani a kan fastocin kamfen dinsa da ke yawo

2023: Gwamnan Kogi ya yi bayani a kan fastocin kamfen dinsa da ke yawo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Ban san yadda aka yi Gwamna Makinde ya warke ba - Karamin Ministan Lafiya

Ya kara da cewa, "Muna so mu bayyana cewa Gwamnan bashi da masaniya a kan hakan. Bai san wata kungiya ko wani mutum da suka buga fostocin ba".

Kamar yadda yace, gwamnan na da tunanin da ba zai sa ya goyi bayan lamarin ba ballantana a irin wannan lokaci da duniya ke fuskantar annobar coronavirus.

Ya kara da cewa, "Gwamnan yana nisanta kanshi daga yakin neman zaben don ya mayar da hankalin yin shugabanci na gari da samar da romon damokaradiyya ga jama'ar jihar Kogi."

"2023 na hannun Ubangiji ne kuma shi ke nadawa tare da saukewa," takardar tace.

Ta kara kira ga jama'a da kada su bar kowanne mutum ko kungiya da za su batar dasu ta hanyar amfani da sunan gwamnan don cimma burinsu na siyasa.

Takardar ta sake tabbatar da cewa burin gwamnan bai wuce ganin tabbatar walwalar jama'ar jihar Kogi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel