Yanzu-yanzu: An sallami mutum 7 da suka warke daga COVID-19 a Legas

Yanzu-yanzu: An sallami mutum 7 da suka warke daga COVID-19 a Legas

- An kara sallamar wasu mutane 7 daga cibiyar killace masu fama da cutukan da ke yaduwa ta jihar Legas

- A yau Alhamis ne Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter

- Ya bayyana cewa dukkan gwaji biyun da aka yi musu na karshe na bayyana cewa sun warke sarai daga cutar

An sake sallamar wasu majinyata 7 da suka warke daga cutar coronavirus daga cibiyar killacewa ta jihar Legas.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne yayi sanarwar a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis kuma jaridar The Nation ta wallafa.

Ya ce, "Jama'a nagari da ke jihar Legas, Ina farin cikin yi muku bushara daga cibiyar killacewa ta Yaba da ke Legas. Muna ta kokarin shawo kan muguwar annobar da ta addabi duniya".

Ya kara da cewa, "A yau ne aka sake sallamar majinyata 7 da suka warke sarai daga muguwar cutar coronavirus. Gwajinsu kashi na biyu kenan wanda yake nuna sun samu waraka".

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 da suka warke daga COVID-19 a Legas
Yanzu-yanzu: An sallami mutane 7 da suka warke daga COVID-19 a Legas
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Na kama mijina yana cin amana ta har su biyu - Matar tsohon gwamnan APC

A wani labari na daban, a ranar daya ga watan Afirilu ne, Ministan lafiya na Najeriya, Dr. Osagie Ehanire ya bayyana cewa da zarar sakamakon gwajin da aka yi wa marasa lafiyar ya nuna sun warke, za a sallamesu daga asibiti.

Dr. Osagie Ehanire ya ce za a sallami wadanda ke kwance a gadajen asibiti ne idan har gwaji ya nuna cewa ba su dauke da kwayar cutar COVID-19 a jikinsu a halin yanzu.

An rahoto Ministan ya na cewa: “An sallami mutane biyar, sun tafi gida. Abin takaicin shi ne Najeriya ta samu mutuwar marasa lafiya biyu (masu cutar COVID-19).”

Ministan kasar ya kara da cewa: “Dukkaninsu su na dauke da wasu cututtukan a jikinsu.”

Daga nan sai ya ke albishir: “Akwai wasu Marasa lafiyan da za a sallama.”

Osagie Ehanire ya nuna cewa za ayi wannan gwaji ne har sau biyu a cikin sa’a 24 zuwa 48. Watau za a yi wa masu gwajin COVID-19 biyu a cikin kwana guda ko biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel