APC: Yadda kyautar mota da kwadayin shugabanci ke barazanar tarwatsa jam'iyya a Gombe

APC: Yadda kyautar mota da kwadayin shugabanci ke barazanar tarwatsa jam'iyya a Gombe

Rashin jituwa ya mamaye jam'iyyar APC reshen jihar Gombe bayan rikicin da ya barke tsakanin wasu manyan jam'iyyar masu fatan zama masu fadi a ji a jam'iyyar.

Rikicin dai ya fara ne a makon da ya gabata bayan an kori dan majalisar tarayya, Usman Bello Kumo.

Wanda ya fitar da wasikar korar kuwa shine Musa Barade, shugaban jam'iyyar APC din na gundumar Kumo ta gabas.

Ya zargi dan majalisar da aikin da zai iya tarwatsa jam'iyyar.

Kumo ya dauka kyautar mota ya bai wa wani mutum mai suna Garba Inuwa Gona, a matsayin kyauta bayan ya zagi Sanata Danjuma Goje a gidan rediyo.

A takardar da aka mika ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, an bayyana rashin ladabi, ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar da kuma kirkirar sashe a jam'iyyar APC din a cikin laifukan Kumo.

Amma kuma, bayan fallasar wasikar ne Shuaibu Adamu ya jagoranci wasu mutane 29 na shuwagabannin jam'iyyar a yankin, inda suka tsame kansu daga lamarin.

Adamu ya zargi Barade da satar sa hannunsu saboda wasu dalilai da shi kadai ya sani.

Daga bisani kuwa, sun dakatar da Barade na watanni shida a kan satar sa hannunsu da yayi a wasikar da ke ta yawo a kafafen yada labarai.

APC: Yadda kyautar mota da kwadayin shugabanci ke barazanar tarwatsa jam'iyya a Gombe
APC: Yadda kyautar mota da kwadayin shugabanci ke barazanar tarwatsa jam'iyya a Gombe
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Gwamnatin Chadi ta yi martani mai zafi a kan zargin da ake mata

Hakazalika, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Akko, Alhaji Waziri Jabbo, ya ce ba a sanar da shugabanin jam'iyyar na karamar hukumar ba a lokacin yanke wannan hukuncin.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta binciko, rikici tsakanin 'yan jam'iyyar ya fara ne tun bayan wani shirin inganta rayuwar matasa da ta mata da aka kaddamar a jihar.

A yayin kaddamar da shirin, wanda ya samu halartar manyan gwamnatin jihar da suka hada da: mataimakin kakakin majalisar tarayya, Ahmed Wase da Gwamna Inuwa, Usman Kumo ya kira gwamnan da shugaban jam'iyyar na jihar.

Kafin zaben 2019 wanda ya kawo Gwamna Inuwa karagar mulkin jihar, Sanata Goje ne shugaban jam'iyyar APC na jihar.

Wannan ne kuwa kololuwar matsayi na jam'iyyar a jihar.

Wasu suna cewa gaskiya hakan ne tunda Inuwa shine gwamnan jihar, toh ya zama shugaban jam'iyyar a jihar idan aka bi kundin tsarin mulkin APC.

Amma kuma wasu sun kalla hakan a matsayin kaskanci ga Sanata Goje.

Hakan ne yasa magoya bayan Goje suka dauka lamarin da zafi har suka fara caccaka tare da zagin Kumo da mukarrabansa.

A lokacin da aka tuntubi shugaban jam'iyyar na jihar, Nitte Amangal ya nuna rashin jin dadinshi a kan korar dan majalisar.

Ya umarci shugabannin jam'iyyar da su daina zagin junansu a gidajen rediyoyin jihar.

Amangal ya kara da cewa za a kafa kwamitin sasanci don kawo maslaha ga mambobin jam'iyyar a jihar.

Sanata Goje da Kumo dai duk 'yan karamar hukumar Akko ne. Za a iya cewa a fannin siyasa a yankin, daga Goje sai Kumo don shine tsohon shugaban karamar hukumar.

Kamar yadda Goje ya bayyana cewa ya bar siyasar takara, akwai yuwuwar Kumo ya karba shugabanci tare da wakilcin siyasa na karamar hukumar Akko da kuma Gombe ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel