COVID-19: Cristiano Ronaldo ya na zaune a gidan £7m da Iyalinsa a Madeira
Fitaccen ‘Dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya killace kansa a wani katafaren gida yayin da cutar Coronavirus ta ke hallaka dubban mutane musamman a Turai da Amurka.
Cristiano Ronaldo ya na labe a cikin wani gida tare da Iyalinsa da wasu ‘Yanuwansa. Wannan gida da ya ci makudan kudi ya na Garin Madeira a kasar Portugal, Mahaifar ‘Danwasan.
A cikin wannan gida da ya ci fam Euro miliyan bakwai, akwai filin kwallon kafa da manyan wuraren wanka har biyu. Ronaldo ya na cikin ‘Yan wasan Duniya da su ka fi kowa kudi.
Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, an kashe kusan Naira 3,192,355,000 wajen gina wannan gida. Wannan gidan ya na da bene hawa bakwai, da kuma duk wasu kayan alatu da jin dadi.
Ronaldo da ‘Yanuwansa sun kebe a wannan gida ne domin gujewa shiga bainar jama’a a daidai lokacin wannan annoba da ta dakatar da kwallon kafa da duk wasu ayyuka a Yankin.
Shekaru hudu da su ka wuce, asalin wannan gida wani dakin ajiye kaya ne. Daga baya ne Ronaldo ya kashe masa wasu makudan kudin da ya canza masa fasali bayan ya mallaki ginin.
KU KARANTA: Ana rade-radin Juventus ta na neman kai da 'Dan wasa Ronaldo
Yanzu haka rahotanni sun bayyana cewa Cristiano Ronaldo da Mai dakinsa Georgina Rodriguez da ‘Ya ‘yansu su na kunshe a wannan gida. Haka zalika tsohuwarsa da ‘Yanuwansa.
Tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid da Manchester United ya baro kasar Italiya ya dawo gida ne a Watan Maris. Ronaldo ya tsero daga Juventus bayan Coronavirus ta barke a kasar.
A wannan gida da Ronaldo ya gyara akwai wurin wanka na zamani watau Jacuzzi. Akai filin yin atisaye. Haka zalika akwai wani dakin ajiye motoci akalla biyar a karkashin kasa.
Kwanakin baya kun ji labarin cewa wasu Abokan aikin Ronaldo a Juventus sun kamu da cutar COVID-19. Daga cikinsu akwai 'Dan wasan gaba Paolo Dybala da kuma Mai dakinsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng